Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ragwanci ke hana wasu mutane neman abinci ta hanyar halal har hakan ya kai su ga shiga miyagun ayyuka.
Shugaban Buhari na magana ne bayan samun rahoton da ke nuna kashi 2.5% na fadin kasar Najeriya a ke amfana da ita wajen aikin noma.
Da ya ke amsa tambaya daga manema labaru yayin bikin babbar sallah a Daura, shugaban ya bukaci 'yan Najeriya su kara dagewa wajen amfana da albarkar fadin kasa wajen neman abin dogaro da kai.
Shugaban Buhari wanda tun a shekarun baya ya zayyana wasu matasan Najeriya da cewa su na da nuna kasala, ya karfafa matsayar ta sa ga nuna ragwanci na daga dalilan shiga miyagun ayyuka.
Karin bayani akan: Garba Shehu, Shugaba Muhammadu Buhari, sallah, daura, Nigeria, da Najeriya.
Kasancewar shugaban ya yi maganar a takaice, mai taimaka ma sa ta fuskar labaru Garba Shehu ya yi karin bayani inda ya fito da batun rahoton da a ka kawowa shugaban na karancin amfani da filayen noma.
Duk da akwai jihohin da ke da zaman lafiya da yanzu haka a ke noma, akwai da dama wadanda shiga daji kan zama tarko mai hatsari.
Hakanan lamunin noma da a ke bayarwa bai faye shiga noman ba sai wasu lamura na daban da su ka hada da gina gidaje da sayen babur ko mota.