Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Miliyan 100 A Bakin Rayukan Daliban Jami'ar Greenfield- Madugun Barayi


Shugaban gungun barayin da su ka sace daliban jami'ar Greenfield a Kaduna Sani Idris Jalingo da a ka fi sani da "Baleri" ya yi barazanar hallaka sauran daliban matukar ba a turo Naira miliyan 100 da baburan Boko Haram 10 ba.

A hirar shi da Muryar Amurka, ta wayar tarho daga daji inda ya ke tsare da daliban 17 bayan kashe 5 daga ciki, Baleri ya ce ranar talata zai dau mummunan matakin matukar ba a turo sakon ba.

Baleri wanda ke nanata cewa da gaske ya ke yi wajen barazanar, ya bayyana cewa yanzu haka akwai mata 15 da maza biyu a hannun su da su ka hada da jikan marigayi sarkin Zazzau Shehu Idris mai suna Hamza.

Yayin da Baleri ke cewa iyayen yaran sun turo mu su diyyar da ta kai naira miliyan 45, ya ce sun sassauto daga wajen Naira miliyan 600 da su ka nema tun farko, yanzu su na bukatar miliyan 100 kuma sun yi amfani da kudin da a ka fara turowa wajen sayawa yaran garin kwaki.

Karin bayani akan: sarkin Zazzau Shehu Idris​, Muryar Amurka, Jami'ar Greenfield, Kaduna, Naira, Baleri, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Madugun barayi Baleri ya ce wannan shi ne wa'adi na karshe da zai bayar na yau litinin din nan.

Har yanzu akwai daliban kolejin kimiyyar gandun daji da ke hannun wasu gungun barayin da hakan ya maida jihar Kaduna mafi fama da kalubalen barayin mutane.

Gwamnatin Kaduna na nanata ba goyon bayan biyan kudin fansa.

Saurari cikakken rahaton a sauti:

Miliyan 100 A Bakin Rayukan Daliban Jami'ar Greenfield- Madugun Barayi
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:21 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG