Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta fara gudanar da babban taronta na kasa a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.
Taron zai zamanto wani mataki na zaben jami’an da za su jagoranci jam’iyyar a matakai daban-daban.
PDP wacce ta fitar da akasarin mukaman bisa amincewar shiyyoyi; na son amfani da nasarar babban taron don shirin babban zabe a 2023.
Wasu rahotanni na nuni da cewa Mr.Iyorchia Ayu daga jihar Binuwai ya kama hanyar zama shugaban babbar jam’iyyar adawa ta PDP yayin da shi kadai ke takarar shugabancin jam'iyyar.
Iyorchia Ayu wanda tsohon shugaban majalsardattawa ne kuma minista a wajen ma'aikatu 4, ya zama dan takara ne bayan janye ma sa da wasu manyan jam'iyyar irin su David Mark, Ibrahim Idris da Jerry Gana su ka yi.
A zantawarsa da gidan talabijin na ARISE, Ayu ya ce har dai ya fara aiki a matsayin shugaban PDP to a shirye ya ke ya dau kowane mataki na sadaukarwa ko da sauka ne daga mukamin in a ka ce don PDP na son mika tikitin takarar shugaban kasa ga arewa ne.
An ruwaito dan kwamitin babban taron gwamnan Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri na cewa kujeru uku kadai a ke da masu hamayya, kuma a na kokarin shawo kan su don samun matsaya.
Mukaman sun hada da na mataimakin shugaban jam’iyyar na kudu, ma'aji na kasa da kuma shugaban matasa.
Fintiri ya kara da cewa ko da an zabi sabbin shugabanni ba za su fara aiki ba sai wadanda ke jagorantar jam'iyyar yanzu sun kammala wa’adin su a ranar 9 ga watan disamba
Tsohon shugaban jam'iyyar Bello Halliru ya ce ya na da kwarin gwiwa da yardar Allah taron zai sharewa PDP hanyar dawowa mulki.
Shi kuma Salisu Hadisu daga Nguru kuma wakili a zaben, ya nuna murnar samun mataimakin shugaban jam'iyyar daga Yobe.
Akalla wakilai 3,600 aka yi has ashen za su halarci babban taron, wanda za a gudanar a ranakun Asabar da Lahadi
PDP wacce ta yi shekara 16 a madafun iko na caccakar APC da cewa ta ba ta wuri don kwarewar shugabanci na PDP kwarewar adawa na APC.
Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El- Hikaya: