Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Alhazan Najeriya NAHCON Ta Bankado Wasu Dillalai Masu Zamba


Hukumar alhazan Najeriya NAHCON ta bayyana bankado wasu kamfanonin dillalan aikin hajji da karbar kudi suna nuna cewa za su kai alhazai don gudanar da aikin hajjin bana.

Wannn na faruwa a shekara ta biyu da Saudiyya ta dakatar da damar maniyatan ketare daga shiga kasar don aikin hajjin sanadiyyar annobar coronavirus.

A sanarwar daga jami'ar labarun hukumar Fatima Sanda Usara ta fitar, ta ce kamfanonin na nuna cewa da izinin NAHCON su ke bugun kirjin za su kai mutane aikin hajjin da VISA ta shiga Saudiyya ba ta aikin hajji ba.

NAHCON ta bukaci jama'a su yi takatsantsan da irin wadannan kamfanoni da ta kwatanta a matsayin masu karambani.

Mun tambayi daya daga cikin masu kamfanonin alhazan Auwal Lalla kan irin wadannan dillalai masu zamba cikin aminci, ya ce lallai ko da an samu kamfanonin, to aikin baban giwa kawai suke yi.

Karin bayani akan: hajjin, hajji, NAHCON, Saudiyya, VISA, Fatima Sanda Usara, Nigeria, da Najeriya.

Hukumar alhazai ta bukaci maniyyata su kwantar da hankali da jiran har al'amura su daidaita don bude zuwa hajjin, haka nan da amfani da hanyar adashen kudin hajji na hukumar musamman ga maniyyata masu karamin karfi.

A yayin da ake shirin hawa Arfa ranar 19 ga watan nan na Yuli, Saudiyya ta fara cafke masu yunkurin shiga wajajen aikin hajji ba da izini ba da cin tarar su riyal dubu 10 wato fiye da Naira miliyan daya kenan.

Saurari rahoto cikin sauti daga Nasiru Adamu El-hikaya:

Hukumar Alhazan Najeriya NAHCON Ta Bankado Wasu Dillalai Masu Zamba
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:44 0:00

Hukumomin Saudiyya Sun Shirya Karban Alhazai a Mina

Hukumomin Saudiyya Sun Shirya Karban Alhazai a Mina
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:05 0:00

XS
SM
MD
LG