Bayanan jami’an gwamnatin Najeriya kan nasarar da a ke samu wajen yaki da ‘yan ta’adda da sauran ‘yan bindiga dadi, na sabawa da irin bayanan da mutanen karkara ke yi.
Yayin da gwamnati ke cewa dakarun tsaro na birkita lissafin miyagun iri, jama’a na cewa miyagun na sauya dabarar hallaka jama’a ne da mallake dukiyarsu.
“Yanzu mu kan kai farmaki ne ga makiyan mu har inda su ke kuma a cikin watanni hudu da su ka wuce zaratan jami’an tsaronmu sun samu gagarumar nasara” inji shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a sashen jawabinsa na ranar ‘yanci.
Shugaban ya nuna murna cewa baya ga nasarar da ya ce jami’an sun cimma, kazalika fiye da ‘yan Boko Haram 8,000 su ka yi saranda a arewa maso gabar.
Shugaban ya ce rundunar soja ta dauki sabbin jami’ai yayin da ya ba wa rundunar ‘yan sanda umurnin a duk shekara har tsawon shekaru 6 ta rika daukar sabbin jami’ai dubu 10.
Mutane a jihohin da musamman a ka datse layukan sadarwa, na nuna bukatar sauya dabara daga jami’an tsaro.
Mansur Abubakar shugaban wata kungiya ce mai taken zaman lafiya da adalci
“Peace and Justice” a arewa maso yamma; ya ce rufe layukan waya na da riba da akasinta.
Shi ma shugaban kwamitin amintattu na gamayyar kungiyoyin arewa Nastura Ashir Sharif ya ce matukar ba a tantance abun da ya ke zahiri ba, gwamnati za ta yi ta zuba kudi ba sakamako mai tasiri.
Akalla dai gwamnatin Zamfara ta dawo da sadarwar salula a Gusau, inda mutan
Munya a Neja ke cewa su ma a bi kadun su don miyagu kan yi kisa a yankin ba hanyar ankarar da jami’ai.
Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El Hikaya daga Abuja: