Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daliban Kaduna: "Mutane Ne Suka Yi Karo-karo Aka Sako Mu"


Rahotanni daga jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa, an sake sako wani rukunin dalibai biyar daga cikin 'yan makarantar kwalejin horar da ilimin gandun daji da aka sace a watan jiya.

Wadanda a ka sako sun hada da mata 4 da namiji daya.

Da ya ke magana ta wayar tarho daya daga wadanda a ka sako mai suna Abdulganiyu Aminu ya ce su na mawuyacin halin yunwa don rashin ingancin abincin da a ke ba su.

Haka nan ya kara da cewa sai da aka yi karo-karo kudin fansar kafin a sako su kuma a kan zabi wadanda su ka fi galabaita ne idan an tashi sakin su.

Aminu ya bukaci gwamnan Kaduna Nasiru El-Rufai ya bi matakan tattaunawa don sako sauran wadanda ke hannun miyagun irin.

Sako rukunin wadannan dalibai su biyar na nufin an saki daliban kwalejin 10 kenan.

Karin bayani akan: Nasiru El-Rufai, jihar Kaduna, Abdulganiyu Aminu, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

A farkon makon nan ne rahotanni suka ce an sako dalibai 5 daga cikin 39 da aka yi garkuwa da su a kwalejin horar da ilimin gandun daji da ke jihar Kaduna.

Kwamishinan tsaron cikin gida Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a cewar rahotanni.

“Sojoji sun sanar da gwamnatin jihar Kaduna cewa, biyar daga cikin daliban kwalejin da aka sace sun kubuta, suna nan can a wani asibitin sojoji ana duba lafiyarsu.” Gidan talbijin na Channels TV ya ruwaito sanarwar mai dauke da sa hannun Aruwan tana cewa.

“Gwamnatin jihar Kaduna, za ta ci gaba da fitar da bayanai kan wannan al’amari.” In jaridar The Nation wacce ta ruwaito sanarwar.

A ranar 12 ga watan Maris aka sace daliban, bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai wani hari a makarantarsu da ke Afaka.

Saurare cikakken rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya:

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG