Kamfanin jirgin sama na MAX ya ba da labarin tashin jirgin sa daya zuwa birnin Bucharest na kasar Romania don kwaso daliban Najeriya da su ka makale a can sanadiyyar mamaye Ukraine da kasar Rasha ta yi.
Masana siyasa na cewa bayan babban taron APC a watan gobe, za a samu karin manyan ‘yan siyasa da za su kafa jam’iyya ta uku mafi karfi da Sanata Rabi’u Kwankwaso ya shimfidawa tabarma.
Barazanar gagarumar zanga-zangar ta kungiyar daliban Najeriya a litinin din nan, ya jawo kira daga wasu iyaye da masu ruwa da tsaki na sara da duba bakin gatari.
masana kimiyyar siyasa da masu sharhi na cewa akwai sauran rina a kaba, bayan sanya hannu da shugaba Buhari ya yi kan sabuwar dokar zabe.
Tuni wannan matakin ya zaburar da wata kungiya mai da’awar sulhu ta APC a Kano karkashin Alh.Yusuf Ado Kibiya da ke shirin sulhunta bangaren gwamna Ganduje da na sanata Shekarau da zummar dakatar da tasirin sabuwar tafiyar.
A ranar 26 ga watan nan na Fabrairu jam'iyyar mai mulki ta APC za ta gudanar da taron nata.
Kungiyoyin matasa magoya bayan jam’iyyar APC sun juya taron rantsar da shugabannin jam’iyyar na jihohi zuwa dandalin kamfen din amsar madafun ikon jam’iyyar.
Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da tsohon gwamnan Imo Sanata Rochas Okorocha sun bayyana niyyar su ta yin takarar shugabancin Najeriya a zaben 2023
Yayin da masu sha’awar takarar shugabancin Najeriya a badi ke kara bayyana muradin su, tsohon shugaban zauren jam’iyyu Yunusa Tanko ya ce za a iya samun garambawul ga tsarin shugabancin Najeriya.
Ya zama mai muhimmanci ‘yan Najeriya su kawar da bambance-bambancen kabilanci, wariya don addini da yanki matukar kasar za ta tsira daga talauci, rashin tsaro da guguwar ‘yan a fasa kowa ma ya rasa.
Alkalin kotun Isma'ila Abdullahi ya tura Jaruma gidan yari don jiran beli a ranar Juma’ar nan mai zuwa.
Wata sabuwar kungiyar masu matsakaicin shekaru a dattawan arewa sun karfafa cewa zabar dattawa masu karancin shekaru a 2023 ne zai kawo maslahar tsaro da tattalin arziki.
Babban daraktan ofishin gwamnonin APC Salihu Lukman wanda ya mika takardar murabus din sa, ya ja hankalin jam’iyyar da cewa babban taron ta na zabar sabbin shugabanni shi ne zakaran gwajin dafin tabuka abun kirki a zaben 2023.
Daya daga mazauna kauyukan karamar hukumar Anka a jihar Zamfara, Murtala Waramu ya ce shi da sauran jama’a sun kirga gawa 52 da ‘yan bindiga su ka yi wa kisan gilla a wani mummunan farmaki da su ka kai.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna nasarorin da kasar ta samu duk da kalubalen tsaro da koma bayan da annobar coronavirus ta haifar wa kasar.
Duk da tsarin dimokradiyya da a ke yi a Najeriya, masu sharhin sun ce ba a samun bambancin manufofin ‘yan siyasa a kowace jam’iyya ba, don tsarin jari hujja da ke nisanta talakawa da masu hannu da shuni ya kulla dangantaka tsakanin su.
Yayin da a ke haramar shiga sabuwar shekara ta 2022, ‘yan Najeriya na nuna matukar damuwa kan shirin gwamnati na janye dukkan tallafin man fetur da hakan zai sa lita ta kai Naira 320-340 daga Naira 162.
Wani kalubale da masana ke hange shi ne irin dambarwar da za a samu a tsakanin manyan jam’iyyu na tsaida ‘yan takarar shugaban kasa tsakanin kudu da arewa.
Majalisar limaman Islama ta yankin Sahel a Afirka wato Rabidatul Islam Fi Biladi Sahel ta kammala taro kan lamuran tsaro a Abuja, babban birnin Najeriya da ganawa ta musamman da kungiyar JIBWIS.
A baya, babban bankin Najeriya ya daina ba da dala ga kasuwar canji inda ya bukaci duk mai son dala ya nufi bankin sa don samun ta kan farashin hukuma.
Domin Kari