A ‘yan kwanakin nan a Abuja a kan wayi gari a ga matasa sun fito da jarkuna kan titi su na sayar da fetur a kasuwar bayan fage inda wasu gidajen man kan rufe amma daga bisani ko can dare sai lamari ya koma daidai.
Duk da ma’aikatan gidajen mai kan ce rashin isowar tankunan dakon mai ne don rufe wata muhimmiyar hanyar da su ke bi, mutane sun shiga fargabar hakan shiri ne kamar yanda a ka saba in za a kara farashin fetur.
Shugaban kamfanin fetur NNPC Mele Kyari Kolo ya bayyana cewa, duk wata gwamnati ta kan kashe tsakanin Naira biliyan 100-120 kan tallafi amma yanzu ba za ta iya ci gaba da kashe makudan kudin ba, za ta goge tsarin a kundin ta.
Talakawa da ‘yan hamayya na caccakar gwamnatin ta APC da ta sha alkawarin daidaita lamura har ma da alwashin da shugaba Buhari ya yi tun kamfen na gugar zanar bai dace lita ta yi tsada ba.
Halima Kajuru wata ‘yar hamaiya ta ce duk alkawuran da a ka dauka ba a gani a kasa ba.
Masana da masu hannu a lamuran fetrur sun sha ba da shawarar kafa kananan matatun fetur din da hakan zai sa a rika tace man da a ke bukata daga cikin gida.
Tuni farashin kayan masarufi ya yi tashin gauron zabi, ballantana a ce litar fetur ta tashi, ba shakka kuncin zai kai kure taya.
Saurari rahoto cikin sauti daga Nasiru Adamu El-Hikaya: