Masana na sharhi kan abubuwan da Najeriya za ta tunkara a siyasance a sabuwar shekarar miladiyya ta 2022 da ke shigowa daga ranar Asabar din nan mai zuwa.
Hukumar zaben Najeriya INEC kan gudanar da zabe akalla wata uku kafin kammala wa’adin wadanda ke kan kujera.
Da ya ke sharhi kan sabuwar shekarar, masanin kimiyyar siyasa na jami’ar Abuja Dr. Abubakar Umar Kari ya ce tuni an shiga harkokin babban zaben 2023 tun kafin ma shekarar 2021 ta kammala yin ban-kwana.
Dr. Kari ya ce cikin hikima, ‘yan siyasa na amfani da duk wata dama ta taro don bayyana muradinsu na takarar kujerar da suke fatar samun tikiti.
Wani kalubale a tabaron Kari shi ne irin dambarwar da za a samu a tsakanin manyan jam’iyyu na tsaida ‘yan takarar shugaban kasa tsakanin kudu da arewa.
Dan siyasa Shamsu Gandi Sokoto ya ce kasancewar akasarin kuri’u na fitowa daga yankin arewa ne, yana da kyau masu zabe su mika zabin su ga Allah maimakon tsayin daka kan wani dan takara kamar yadda a ka yi ga shugaba Buhari.
Shi kuma jigon APC mai mulki Faruk Adamu Aliyu ya yi fatar lamuran tsaro su inganta kafin lokacin zaben musamman a arewa maso yamma inda matsalar ta fi ta’azzara.
Za a iya cewa an samu ‘yar sararawa ta sauya sheka daga adawa zuwa jam’iyya mai ci da hakan ke nuna akasarin ‘yan siyasa na sake lissafi don kar a samu sake reshe ko lissafin mai cewa 6 wani ya ce 9 ce bisa gefen da mutum ke duba lambar.
Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El Hikaya: