‘Yan siyasar biyu daga babbar jam’iyyar adawa PDP da jam’iyyar APC mai mulki na cikin fitattun masu rike da mukamai 5 da su ka nuna sha’awar karbar ragama daga shugaba Buhari.
Wadanda su ka ayyana yin takara zuwa yanzu baya ga wadannan biyu, sun hada da tsohon gwaman Lagos Bola Ahmed Tinubu, gwamnan Ibonyi Dave Umahi, tsohon gwamnan Abia Orji Uzo Kalu da wanda ba ya jerin masu mukamai Barista Adewole Adebayo na kafar labarun Kaptan; sai kuma masu kamfen don neman takarar mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo a APC da na tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a PDP.
Ba a yi mamakin niyyar ayyana takarar Tambuwal ba tun da ya gwada neman tikiti a 2019 kuma bai gamsu da salon mulkin shugaba Buhari ba.
Ba mamaki Tambuwal wanda ya zama kakakin majalisar wakilai ba ya sha’awar takarar majalisar dattawa kamar yadda akasarin masu gama wa’adin gwamna ke yi.
Daidai lokacin da Okorocha ke niyyar ayyana takarar, hukumar EFCC ta gabatar da caji a kan sa a babbar kotun tarayya ta hada kai da wasu a badakalar Naira biliyan 2.9.
Okorocha wanda ya ja aya a Alkur’ani da ke nuna adalci da ya ke bukata kasar ta yi; ya shawarci ‘yan uwansa Igbo da cewa ba wanda zai ji tsoron su ya ba su mulki, don haka gwagwarmayar su ce za ta sa su samu ta hanyar magana da sauran jama’a.
Zuwa yanzu ‘yan kudu su ka fi yawa a masu niyyar takara a zahiri.
In za a tuna, shugaba Buhari a zantawa da gidan talabijin na Channels ya nuna ba zai bayyana sunan dan takarar sa ba don kar a kulla ma sa makarkashiya duk da ya nuna ba damuwar sa ba ce zaben mai zuwa.
Da alamu za a samu karin fahimtar yadda lamuran siyasar za su dosa bayan babban taron APC na zaben sabbin shugabanni a ranar 26 ga watan nan na Fabrairu.
Saurari rahoto cikin sauti daga El-Hikaya: