Daliban dai a tutar kungiyar su NANS a takaice na son matsa lamba ga kungiyar malamai ASUU da gwamnati su daidaita don dakatar da yajin aikin malaman.
Zuwa karshen makwan nan, ba wata alama da ke nuna kungiyar daliban za ta dakatar da batun zanga-zangar, don haka kiraye-kiraye su ka fara yawa na takatsantsan don kar hakan ya zama damar bata gari ta shafar zaman lafiya.
Shugaban kungiyar daliban Sunday Adedayo ke karfafawa daliban guiwa su fito ranar litinin, su datse dukkan manyan titunan Najeriya don biyan muradin na su.
Adedayo ya nuna matsalar kan shafi ‘ya’yan talakawa ne da kan shiga jami’o’in gwamnati, don haka ba a maida hankali ga warware kalubalen ba.
Tsohuwar minister ilimi Aisha Jibir Dukku ta yi kira ga daliban su maida wuka kube, don zanga-zangar ba ita ce hanyar maslaha ba.
Hakanan shi ma daya daga iyayen yara Mustapha Bomo daga Zaria, ya nuna fargaba kan sakamakon da zanga-zangar za ta haifar.
Kungiyar ASUU na cigaba da yin yajin aikin gargadi na tsawon wata daya bayan na kwana daya da zummar matsa lamba ga gwamnati ta aiwatar da yarjejeniyar da ta kawo karshen dogon yakin aikin wata 9 a bariya.
Saurari cikakken rahotonn cikin sauti: