Jami’in labarun kamfanin na MAX Ibrahim Dahiru ya ce jirgin na da girman da zai iya daukar fiye da fasinja 500.
Dahiru ya ce zuwa safiyar jumma’ar nan a ke sa ran dawowar jirgin don an kammala rajistar fasinjojin da zai dauko da hakan ya nuna ba a fargabar samun wani jinkiri.
Kazalika Dahiru ya ce iya aikin da a ka ba wa kamfanin na zuwa Romania ne.
Daliban da sauran ‘yan Najeriya na kasashe da ke makwabtaka da Ukraine da su ka hada da Poland, Romania, Slovakia, Hungary har ma da wasu da su ka makale a yankin da Rasha ke da shi.
In za a tunawa gwamnatin Najeriya ta ware dala miliyan 8.5 don aikin wannan jigila da amfani da kamfanoni biyu da su ka hada da MAX da AIR PEACE.
Saurari cikakken rahoton a cikin sauti: