Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Gwamnoni A Jam’iyyar APC Ba Ta Kare Ba


Babban daraktan ofishin gwamnonin APC Salihu Lukman wanda ya mika takardar murabus din sa, ya ja hankalin jam’iyyar da cewa babban taron ta na zabar sabbin shugabanni shi ne zakaran gwajin dafin tabuka abun kirki a zaben 2023.

Lukman ya yi gargadin ne a wata sanarwa gabanin daukar matakin yin murabus ta hanyar mika takarda ga shugaban kungiyar gwamnonin APC Atiku Bagudu.

Takaddamar ta samo asali ne ga yadda Salihu Lukman ke ganin gasar rike madafun iko a jam’iyyar na neman kawo damuwa ga dorewar mulkin jam’iyyar bayan kammala wa’adin mulkin shugaba Buhari a badi.

Lukman ya bsayyana cewa, ra’ayin na sa ne bai shafi na ofishin kungiyar gwamnonin ba, ya nuna yanayin da jam’iyyar ke tafiya a kai, ya yi daidai da dalilan da su ka saka aka kawar da tsoffin shugabannin jam’iyyar karkashin Adams Oshiomhole.

Ba mamaki zargin tsawaita lokacin gudanar da babban taron zuwa watan yuni ya kau, don kungiyar gwamnonin ta ba da tabbacin gudanar da taron a watan gobe.

Shugaban kungiyar gwamnonin Atiku Bagudu ke bayyana shirin gudanar da babban taron amma ya ce hakkin ayyana ranar a watan gobe wato Fabrairu na wuyan kwamitin riko na jam’iyyar karkashin gwamna Mai Mala Buni.

Dattawan jam’iyyar irin su Danmalikin Kebbi Musa Abubakar sun bukaci jam’iyyar ta gyara matsalolin da su ke tasowa don gudun yin sakiyar da ba ruwa.

Jin wannan ya sa ‘yan jam’iyyun hamayya wasa wukar adawa don neman kawar da APC daga mulki a 2023 musamman in bango ya tsage. Yunusa Tanko na jam’iyyar NCP wanda ya taba takarar mataimakin shugaban kasa ya baiyana wannan muradi.

Idan ba an kammala babban taron lafiya da samun shugaba da zai iya samun karbuwa, ba za a gano makoma ko alkiblar APC ba

Abuja ta cika da manyan hotunan a jikin alluna na masu son takara da akasarin su tsoffin gwamnoni ne irin su Tanko Almakura, Abdul’aziz Yari, Ali Modu Sheriff, George Akume da sauran su.

Saurari rahoto cikin sauti daga Nasiru Adamu El-Hikaya:

Rikicin Gwamnoni A Jam’iyyar APC Ba Ta Kare Ba
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG