Tawagar malaman da ta kai mutum 50 ta yi zama na musamman na bita kan lamuran magance kalubalen tsaro da hukumar sirri ta Najeriya.
Malaman wadanda su ka hada da kwararru kan yaki da ta’addanci, sun nuna gamsuwa ga irin nasarar da a ka samu ta bitar da za ta taimaka wajen cusa akida mai kyau ga matasa da kan tsinci kansu a rudin miyagun iri wajen aukawa ta’addanci da sunan yada addinin musulunci.
Shugaban majalisar Dr. Abubakar Walar daga Chadi da sakataren ta Lakhamisi Bazzaz daga Aljeriya sun cirawa Izala hula don yanda ta kan yi amfani da wa’azi da bude makarantu don koyar da akidar musulunci daga koyarwar magabata.
Hakanan jagororin na Rabida ta Sahel sun nuna matukar farin ciki ga labarin aikin gina jami’a mai suna Assalam da JIBWIS ke yi a Hadeja jihar Jigawa; ba ya ga kafa manyan kafafen labaru na wa’azantarwa Manara TV da Manara Rediyo.
Da ya ke maraba da bakin shugaban JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau da shugaban majalisar malamai Dr. Ibrahim Jalo Jalingo ya wakilta, ya ce da irin wannan tattaunawa za a rika gano bakin zaren rigakafin fitina tun kafin ta girma.
Najeriya na fama da fitinar ta’addancin ‘yan Boko Haram da kan fake da sunan addini tun 2009 amma su kan buge da kisan gilla ga wadanda ba su yi musu laifin komai ba.
Yanzu kuma ga sabuwar fitina da ke tinkarowa ta kabilanci da addinin musulunci ya haramta.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: