Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Sa A Tsare Jaruma A Gidan Yari Kan Zargin Batancin Da Ta Yi wa Wani Attajiri


Jaruma, hagu (Twitter/Jaruma Empire) Ned Nwoko, dama (Instagram/Ned Nwoko)
Jaruma, hagu (Twitter/Jaruma Empire) Ned Nwoko, dama (Instagram/Ned Nwoko)

Alkalin kotun Isma'ila Abdullahi ya tura Jaruma gidan yari don jiran beli a ranar Juma’ar nan mai zuwa.

Wata babbar kotun yanki a Abuja, babban birnin Najeriya, ta tura shahararriyar mai sayar da “kayan-mata” Hauwa Muhammed wacce a ka fi sani da jaruma gidan yari bayan gurfanar da ita a gaban kotun.

Ana tuhumar Jaruma ne da laifin batawa wani dan kasuwa mai suna Mr.Ned Nwoko suna.

Nwoko dai ya taba zama dan majalisar wakilan Najeriya daga 1999-2003 inda daga nan a ka ga ya na lamuran kasuwanci, bayyana a jirginsa mai tsada da daukar hotuna da matansa da ‘ya’yan sa.

Cikekken sunan sa Yarima Ned Munir Nwoko daga jihar Delta.

Takaddamar ta fara ne daga zargin da Jaruma ta yi wa Nwoko na cewa maganin da ta ke sayarwa ne ya yi tasiri a kan sa har matar sa ‘yar kasar Maroko ta rabu da shi.

Nwoko ya shigar da korafi gaban rundunar ‘yan sanda ta Abuja na neman a bi kadinsa ga zargin bata ma sa suna da Jaruma ta yi kuma a binciki sahihancin maganin da ta ke sayarwa da ya ce ba tare da lasisi ba.

A gaban kotun mai shigar da kara na ‘yan sanda E.A. Enegbenoise ya bukaci alkali ya ba da dama a ajiye Jaruma a ofishin ‘yan sanda don jiran beli inda lauyan ta kuma James Odibe ya bukaci a ba da belin ta ne nan take tun da sananniya ce.

Alkalin kotun Ismaila Abdullahi ya tura Jaruma gidan yari don jiran duban beli a Juma’ar nan mai zuwa inda ya tsaida ranar 23 ga watan gobe don ci gaba da shari’ar.

Zargin da Nwoko ya shigar ya nuna Jaruma ta bata ma sa suna ta hanyar wallafa bayanai a shafinta na Instagram mai yawan mabiya, ta na mai cewa tasirin kayan mata da ta ke sayarwa ya ke aiki a jikin ‘yar lelen Nwoko wato daya daga matansa ‘yar fim din Nollywood Regina Daniels wanda ya sa ya zama mijin-ta-ce sai yanda ta ga damar juya shi.

Haka nan Jaruma ta nuna takaicin yanda a yawan shekarun Nwoko ya ci zarafin matarsa ‘yar Maroko mai suna Laila Charani.

Nwoko wanda ke da ‘ya’ya da yawa har ma wadanda Charani ta haifa ma sa, ya musanta zargin na Jaruma ya na mai cewa halin fantamawa ne na Charani a yayin ziyarar shakatawa a London ya kawo sabanin da ba zai sulhuntu ba a tsakanin su, don Charani ta watsar da ‘ya’yan a hotel ta tafi yawon kulob da kashe dukkan kudin saye-saye da ya ba ta ba tare da sayawa yaran komai ba.

Jaruma wacce ‘yar asalin jihar Gombe ce ta fara tallar kayan mata a 2010 amma sai a 2016 sunan ta ya yi tambari bayan yayata cewa goron-tula na taimakawa mata wajen mallakar maza.

A kwanakin baya jaruma ta zargi wani matashin dan siyasa da cin amanar ta bayan taimakawa ta yi ma sa jagorar sayar da wani gida kan miliyoyin Naira inda ta ce ya ki cika alkawarin ba ta kason dillanci na Naira miliyan 13.

Hauwa Muhammed ta yi barazanar sa kafar wanda daya da dan siyasar ta na mai cewa ba wanda za ta ragawa k omeye matsayin sa a wajen ta matukar ya ci amanar ta.

An yi amanna cewa Jaruma ta sha gaban kowace mace mai tallar kayan-mata a Najeriya inda mutane birjik kan yi magana da zarar ta yi wani dan rubutu wanda hakan ya sa ta kan samu nasarar kafar labarun yanar gizo ga duk wanda ya fada tarkon ta. Yanzu haka ta na da mabiya miliyan 1.3 a kafar Instagram.

Tuni labarin tura Jaruma gidan gyaran hali na Suleja domin jiran beli ya zama muhimmin labari a manyan kafafen labaru musamman jaridu a Najeriya inda alamu ke nuna kafar labarum Instagram ta mabiyan Jaruma za ta cika da martani iri-iri na ra’ayoyi mabambanta.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG