Batun dorewar zaman lafiya da hadin kan kasa shi ne ya dauki hankalin da dama daga cikin wadanda suka halarci bikin cika shekara 80 da zagayowar ranar haihuwar tsohon shugaban mulkin soja a Najeriya Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya.
A cewar Iliya Garba, hadimi ga kwamishinan, an sako shi ne bisa kokarin iyalansa ba tare da biyan kudin fansa ba.
Wasu 'yan bindiga sun hallaka akalla mutum biyu tare da jikkata wasu da dama, da kuma yin garkuwa da shugaban jam'iyyar APC na yankin Arewacin jihar Neja a Najeriya.
Hukumomi a jihar Kwaran Najeriya na gudanar da bincike akan kisan wata yarinya mai suna Fatima Abdulkadir ‘yar kimanin shekaru 18 ta hanyar kona ta da wuta.
Gwamnatin jihar Nejan Najeriya ta sanar da rufe wasu makarantu guda 31 saboda matsalar rashin tsaro da ta addabi jihar.
Daya daga cikin daliban makarantar Islamiyyar Salihu Tanko a Tegina dake hannun ‘yan bindiga a jihar Nejan Najeriya da Allah ya bata sa'ar tserewa, ta ce ta sha bakar azabar yunwa da bugu da kuma tafiyar kasa a lokacin da take hannun 'yan bindiga.
Gwamnatin jihar Nejan Najeriya ta sanar da korar ma'aikatanta guda 328 daga bakin aiki saboda samunsu da laifuffuka daban-daban da suka karya dokokin aikin gwamnati a jihar.
Gwamnatin jihar Nejan Najeriya ta ce zata sanya karfi wajen kubutar da yaran makarantar Islamiyyar Salihu Tanko su 148 dake garin Tegina wadanda ke hannun ‘yan bindiga a halin Yanzu.
Bayanai dai sun nuna cewa jami’an tsaron ‘yan bangar sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suka tunkari ‘yan bingar a kokarinsu na kwato wasu shanu.
Yan bindigar da suka yi garkuwa da daliban Islamiyyar Salihu Tanko 148 a garin Tegina ta Karamar Hukumar Rafin jihar Nejan Nigeria sun ce sai an biya Naira miliyan 150 a matsayin kudin fansa kafin su sako yaran da akasarinsu yan kasa da shekaru 13 ne.
Hukumar Makarantar Islamiyyar Salihu Tanko, dake garin Teginan Jihar Nejan Najeriya da 'yan bindiga suka yi garkuwa da dalibanta a ranar Lahadin da ta gabata, ta tabbatar da mutuwar 2 daga cikin iyayen daliban sakamakon tashin hankalin sace masu 'ya'ya.
Kimanin mutum 18 wasu mahara suka kashe yayin da 15 suka jikkata a garin Beri dake cikin jihar Nejan Najeriya.
A kokarin yaki da 'yan bindiga da suka addabi jihar Nejan Najeriya, gwamnatin jihar ta kaddamar da wata rundunar sintiri da ta baiwa horo na musamman ta yadda za ta yi yaki da wadannan 'yan bindiga.
Dubban masu zanga-zangar nuna takaicin rashin tsaro a jihar Nejan Najeriya, sun kwashe sa'o'i da dama, inda suka rufe babbar hanyar mota da ta tashi daga Kaduna zuwa babban birnin tarayya Abuja.
Wasu mahara dauke da manyan bindigogi akan babura, sun kashe Sardaunan Kontagora tare da wasu mutane a jihar Neja dake arewacin Najeriya.
An kashe Sojojin Najeriya guda uku a wani hari da wasu 'yan bindiga su ka kai a jihar Neja dake Arewaacin kasar.
Da yammacin ranar litanin nan ne masu aikin ceto suka kammala aikin lalubo mutanen da jirgin ruwan kwale kwale ya kife da su a garin Galkogo dake gaban ruwan Shiroro ta jihar Nejan Nigeria.
Gwamnatin jihar Neja ta sanar da hana duk wasu bukukuwan sallah da suka hada da hawan dawakai a bikin karamar sallah da za a gudanar mako mai zuwa.
Daruruwan mutane sun tsere daga garin Shadadi a yankin karamar hukumar Mariga dake cikin jihar Nejan Najeriya bayan da 'yan bindiga suka aukawa garin.
Wasu mutane da ake zaton 'yan bindiga ne sun yi awon gaba da shugaban kungiyar makiyaya ta Miyatti Allah na Jihar Kogin Nigeria.
Domin Kari