Gwamnatin jihar Nejan ta ce ta samar da wadannan 'yan sintiri ne da za su gudanar da aiki da jami'an tsaro, abin da ta ce zai taimaka a kokarinsu na kawar da 'yan ta'adda da suka addabi jihar Nejan in ji Kwamishinan kananan Hukumomi da Masarautu na jihar Barista Abdulmalik Sarkin Daji da ya Wakilci Gwamnan Jihar a wajan kaddamar da wadannan 'yan sintiri.
Kwamishinan 'yan sanda na jihar Nejan Alh. Adamu Usman, ya ce sun zabo 'yan sintirin ne daga kungiyoyin dake taimakawa jami'an tsaro a jihar kuma sun ba su horo kamar yadda ya kamata.
Nasiru Muhammad Manta shi ne kwamandan kungiyar 'yan banga a jihar Nejan ya kuma ce za su yi aiki domin tabbatar da ganin bayan 'yan ta'adda da suka addabi jihar Nejan.
A baya, gwamna Abubakar Sani Bello, ya sha alwashin ganin an samar da irin wannan kungiya ta 'yan sintiri, a wani kokari da ya ce gwamnatinsa na yi don ganin karafaf matakan tsaro a jihar.
Ya kuma kara da cewa, 'yan sintirin, za su yi aiki ne kafada da kafada da jami'an tsaro.
A yanzu al'ummar jihar Nejan na cike fatar ganin samar da wadannan 'yan sintiri ya kawo canji ta fuskar tsaron.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: