Ofishin sakataren gwamnatin jihar Neja, Alhaji Ahmed Ibrahim Matane, shine ya fitar da wata sanarwa dake nuna cewa gwamnati ta dauki wannan mataki ne dalilin rashin tsaro da ya addabi jihar, kuma dokar ta shafi dukkan manyan masarautun jihar takwas.
Tun farko dai kafin wannan sanarwar masarautar Minna ta bada sanarwar soke hawan karamar sallah.
Kwamishinan gandun daji na jihar Neja, Alhaji Haruna Nuhu Dukku, ya ce ‘yan fashin daji sun tarwatsa garuruwa da dama a yankin Rijau, dake masarautar Kontagora.
Yanzu haka dai dubban ‘yan gudun hijira da ‘yan bindiga suka raba da muhallansu za su gudanar da bukukuwan karamar sallah daga sansanonin da suke fakewa.
Domin karin bayani saurari rahotan Mustapha Nasiru Batsari.