Bayanai dai sun nuna cewa maharan sun auka wani kamfanin yin hanya ne mallakar wasu ‘yan kasar China dake kauyen Liballe a yankin karamar hukumar Magama.
A wani taron manema labarai bayan kammala wani taro akan matsalar tsaron a jihar Nejan gwamnan jihar Alh. Abubakar Sani Bello ya tabbatar da kashe wadannan sojojin a hannun 'yan bindiga.
Gwamnan ya kuma taya iyalensu ta'aziya yayin da ya bayyana cewa, ba za su fasa yaki da 'yan bindiga ba a jihar Neja ba.
Lamarin ya faru ne cikin daren Litinin wayewar garin Talata kamar yadda shugaban karamar hukumar ta Magama ya tabbatar.
Karin bayani akan: jihar Neja, 'Yan Bindiga, Sojojin Najeriya, Muryar Amurka, China, Nigeria, da Najeriya.
Hon. Sifiyanu Yahaya Ibeto ya yi karin bayani inda ya shaida wa Muryar Amurka cewa, ya ga jami'an tsaro biyu da aka kashe sannan wasu Fulani da ake zaton barayi n.
Amma kuma alamu na nuna cewa ba hakan ba ne, gannin cewa an ga buhun masara tare da su kamar su na da niyyar kai nika.
Yayin taron manema labaran, Gwamna Bello ya kuma kara da cewa sun samu nasarar mayar da wasu 'yan gudun hijira garuruwansu bayan lafawar al’amurra a wasu garuruwa kimanin 30 kuma sun dauki matakai na kariya don ba su damar noma cikin natsuwa.