Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubban Masu Zanga-Zanga Sun Rufe Hanyar Kaduna Zuwa Abuja Saboda Rashin Tsaro


Masu Zanga-Zanga Sun Rufe Titin Abuja Zuwa Kaduna A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:46 0:00

Masu Zanga-Zanga Sun Rufe Titin Abuja Zuwa Kaduna A Najeriya

Dubban masu zanga-zangar nuna takaicin rashin tsaro a jihar Nejan Najeriya, sun kwashe sa'o'i da dama, inda suka rufe babbar hanyar mota da ta tashi daga Kaduna zuwa babban birnin tarayya Abuja.

Lamarin ya faru ne a daidai dai dai sabon Wuse dake yankin karamar hukumar Tafa a jihar Nejan.

Bayanai dai sun nuna cewa zanga-zangar ta rikide zuwa tarzoma kuma an shirya ta ne domin nuna takaici akan yadda ‘yan bindiga ke ci gaba da sace mutane domin neman kudin fansa a yankin.

Zanga-zangar Nuna Takaicin Rashin Tsaro A Jihar Nejan Najeriya
Zanga-zangar Nuna Takaicin Rashin Tsaro A Jihar Nejan Najeriya

Daya daga cikin masu zanga-zangar ya ce suna bukatar a sako masu sama da mutum 50 da aka sace masu a ranar Lahadi 23 ga watan Mayu.

Karin bayani akan: jihar Nejan​, Kaduna, zanga-zangar, Nigeria, da Najeriya.

Gwamnatin jihar Nejan dai ta ce tana sane da wannan zanga-zanga kuma tana daukar matakai akan matsalar rashin tsaron, in ji Sakataren Gwmnatin jihar Nejan Alhaji Ahmed Ibrahim Matane.

Zanga-zangar Nuna Takaicin Rashin Tsaro a Jihar Nejan Najeriya
Zanga-zangar Nuna Takaicin Rashin Tsaro a Jihar Nejan Najeriya

Zanga-zangar dai ta kai ga kona ofishin ‘yan sanda a yankin, sai dai har ya zuwa Lokacin hada wannan rahoto rundunar ‘yan sandan jihar ba ta ce komai ba, kuma kokarin samun kakakin ‘yan sandan Wasiu Abiodun ya ci tura.

Amma Sakataren Gwamnatin jihar Nejan Ahmed Matane ya ce za su hukunta masu daukar doka a hannunsu.

Saurari rahoto cikin sauti daga Mustapha Nasiru Batsari:

Dubban Masu Zanga-Zanga Sun Rufe Hanyar Kaduna Zuwa Abuja Saboda Rashin Tsaro
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG