Rahotanni daga jihar Nejan Najeriya na nuna cewa ‘yan bindiga sun hallaka wasu jami’an tsaron ‘yan banga su kimanin 30 a lokacin wata arangama.
Bayanai dai sun nuna cewa jami’an tsaron ‘yan bangar sun gamu da ajalinsu ne alokacin da suka tunkari ‘yan bingar a kokarinsu na kwato wasu shanu da suka sata daga yankin karamar hukumar Magama a cewar daya daga cikin ‘yan bangar da ya tsallake rijiya da baya.
Shugaban karamar hukumar Magama Hon. Sifiyanu Ibeto, ya ce ya zuwa lokacin da aka tuntube shi akan batun aukuwar lamarin ba su kammala tattara gawarwakin ba.
Kawo lokacin hada wannan rahoto dai babu wani karin bayani daga rundunar ‘yan sandan jihar Nejan domin kuwa kokarin samun kakakin ‘yan sandan DSP Wasiu Abiodun ya ci tura.
Karin bayani akan: Salihu Tanko, jihar Neja, jihar Nejan, Nigeria, da Najeriya.
Sai dai gwamnatin jihar Nejan, ta tabbatar da aukuwar lamarin kamar yadda sakataren Gwamnatin jihar Ahmed Ibrahim Matane ya shedawa manema labarai.
A halin da ake ciki dai daliban makarantar Islamiyyar Salihu Tanko dake garin Tegina har yanzu suna daji a hannun ‘yan binbinga. Amma Gwamnatin jihar Nejan ta ce tana can tana kokarin kubutar da su.
Saurari rahoto cikin sauti daga Mustapha Nasiru Batsari: