Aisha Alasan 'yar kimanin shekaru 12 wadda a yanzu haka take fama da rashin lafiya a sakamakon wahalar da tasha na tsawon sama da kwanaki 30 a hannun wadannan ‘yan bindiga ta ce sau daya ne ake ba su abinci a yini a lokacin da ta ke bayani.
Daya daga cikin iyayen yaran mai suna Fatima ta ce suna cikin wani yanayi na tashin hankali yanzu.
Shi kuma Shugaban makarantar Abubakar Garba Alhasan ya ce kuma babu wani ci gaban da aka samu tun bayan kubutowar 2 daga cikin yaran a makon jiya.
Karin bayani akan: ‘yan bindiga, jihar Nejan, Abubakar Sani Bello, daliban, Nigeria, da Najeriya.
Amma Gwamnatin jihar Nejan dai ta sha nanata cewa tana iya kokarinta domin ganin ta kubutar da wadannan yara.
Gwamnan jihar Nejan Alhaji Abubakar Sani Bello da kansa ya kaddamar da wata runduna ta musamman a yankin da aka sace daliban inda ake yin taka- tsantasn domin ganin an kubutar da yaran lafiya.
Saurari rahoto cikin sauti daga Mustapha Nasiru Batsari: