Tun a ranar Asabar din karshen mako ne jirgin ruwan kwale kwalen ya kife da kimanin mutane 100 da akasarinsu yan gudun hijira ne da ke komawa garuruwansu bayan samun saukin hare haren 'yan bindiga da suka addabi yankin na shiroro.
Shugaban Hukumar Bada Agajin Gaggawa a jihar Nejan Alh. Ibrahim Inda yace sun gano gawarwakin mutane 32 bayan haka kuma yara 2 sun bace, har yanzu kuma ba'a gano gawarwakin su ba.
Mamman Sarki ya rasa yan’uwansa guda shidda a hadarin jirgin ruwan da ya ce suna hanyar komawa gida ne bayan samun saukin hare haren 'yan bindiga da suka koro su daga gidajensu.
Wannan matsala ta hadarin jirgin ruwan kwale kusan duk shekara tana haddasa asarar rayukkan jama'a.
To amma shugaban Hukumar bada agajin a jihar Neja Alh. Ibrahim Inda yace gwamnati na daukar matakin rage asarar rayukka sakamakon hadurran jiragen ruwan musamman ma a lokacin damina.
Saurari cikakken rahoton a sauti: