Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan bindiga Sun Kashe Mutum 18 A Sabon Harin Da Suka Kai Jihar Neja


Kimanin mutum 18 wasu mahara suka kashe yayin da 15 suka jikkata a garin Beri dake cikin jihar Nejan Najeriya.

'Yan bindigar dai sun auka garin na Beri ne dake yankin karamar Hukumar Mariga da sanyin safiyar Litinin, inda bayanai su ka nuna cewa sun share sa’o’i uku suna tabka gumurzu a tsakaninsu da mutanen gari da 'yan banga da kuma wasu jami’an tsaro.

'Yan bindigar sun kashe babban malamin garin mai suna Malam Bello Beri tare da kona karamin ofishin 'yan sanda na garin.

Karin bayani akan: Beri, 'Yan bindiga, Jihar Neja​, Jihar Nejan, Nigeria, da Najeriya.

Gwamnatin Jihar Neja​ ta tabbatar da kai harin amma tace bata da tabbacin adadin mutane da aka kashe, inji Sakataren Gwamnatin Jihar Nejan Alh. Ahmed Ibrahim Matane.

Har ya zuwa lokacin hada wannan rahoton dai babu wani karin haske daga rundunar 'yan sandan Jihar Neja​.

Saurari cikakken rahoton a cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:30 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG