Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za Mu Yi Amfani Da Karfi Don Kubutar Da Daliban Tegina - Gwamnatin Neja


‘Yan Bindiga
‘Yan Bindiga

Gwamnatin jihar Nejan Najeriya ta ce zata sanya karfi wajen kubutar da yaran makarantar Islamiyyar Salihu Tanko su 148 dake garin Tegina wadanda ke hannun ‘yan bindiga a halin Yanzu.

A yanzu haka yaran sun kwashe kimanin kwana 23 a hannun wadannan ‘yan bindiga ba tare da samun nasarar kubutar da su ba,

Gwamnan jihar Nejan Alhaji Abubakar Sani Bello wanda ya je garin Kagara domin jajantawa iyayen daliban Islamiyyar da kuma kaddamar da wasu jami’an tsaro na musamman a ranar Litinin, ya ce akasarin masu aikata ta’addacin nan fa ba yan Najeriya ba ne, saboda haka bai kamata a saurara masu ba.

Sai dai shugaban makarantar Islamiyyar Malam Abubakar Garba Alhassan ya ce suna da fargaba ga matakin Gwamnati na neman kwato yaran da karfin bindiga saboda gudun salwantar da rayukkansu.

‘Yan Bindiga
‘Yan Bindiga

A halin da ake ciki, shugaban makarantar Islamiyyar ya ce 3 daga cikin malaman dake hannun ‘yan bindigar sun samu nasarar kubutowa.

A wani labarin kuma Gwamnatin Jihar Nejan ta mika sakon ta’aziyya ga iyalan ‘yan banga kusan talatin da ‘yan bindiga suka kashe a karshen makon nan.

Gwamnan jihar Nejan ya ce lamarin abin takaici ne kuma za su tallafawa iyalansu.

Saurari rahoto cikin sauti daga Mustapha Nasiru Batsari:

Za Mu Yi Amfani Da Karfi Don Kubutar Da Daliban Tegina - Gwamnatin Neja
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:37 0:00


Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG