Gwamnatin jihar Nejan Najeriya ta ce ta na shirin tafiya kotu idan har gwamnatin Najeriya ta ki ba ta kaso 13 na kudaden da ake samu daga tashoshin samar da hasken lantarki dake jihar.
Yanzu haka dai matsalar rashin tsaro na ci gaba da jefa daruruwan mazauna yankunan karkara cikin tashin hankali a sassa dabam daban na jihar Neja a Najeriya.
Kungiyar Zabarmawa mazauna Najeriya ta nuna rashin amincewa da kai harin soja a Nijar bayan juyin mulki da sojoji suka yi a watan Yuli.
Masana harkokin tsaro a Nijeriya na ci gaba da nuna shakku akan matsayin da gwamnan Jihar Neja ya dauka na cewa yana son yin sulhu da ‘yan bindiga da ke ci gaba da hallaka jama’a a jihar.
Bayanai na nuni da cewa, wasu ‘yan bindiga sun yi wa jami’an tsaron Najeriya kwanton bauna a yankin Zangeri da ke kan iyakar kananan Hukumomin Rafi da Wushishi, a daidai lokacin da jami'an sojojin ke kokarin hana ‘yan bindigar wucewa da daruruwan shanun jama’a da suka koro.
Tun kafin isowar damunar, hukumar hasashen yanayi ta Najeriya ta yi gargadin samun ambaliyar ruwa a kananan hukumomi da dama na kasar a ciki har da na jihohin Nejan.
Duk da cewa suna kusa da tushen wutar lantarki na Kainji dake jihar Neja a Najeriya, garuruwan da suke gabar ruwan da ke samar wutar lantarki a kasar suna zaune ne cikin duhu.
Bayan kammala aikin Hajjin bana na shekara ta 2023 a ranar jumma’a aka yi jifan shaidan na karshe, yanzu hankalin Alhazai ya karkata zuwa gida tare da duba nasarori da kuma matsalolin da aka samu a lokacin aikin Hajjin.
Alhazan duniya kimanin milIyan biyu ciki har da 'yan Najeriya ne ke shirin hawan Arafah a ranar Talata, yayin da wasu ‘yan Najeriya ke da burin yi wa kasar addu’ar zaman lafiya.
Lamarin rashin tsaron dai ya kara ta'azzara a ‘yan kwanakin nan a jihar Nejan Najeriyar, al’amarin da ya jefa dubban mazauna yankunan karkara cikin yanayi na tashin hankali.
Wani Mazaunin yankin da lamari ya faru Malam Muhammad Sani ya ce jirgin kwale-kwalen ya dauko wasu ‘yan biki ne daga kauyen Boti na yankin karamar hukumar Patigi ta jihar Kwara.
Masu ruwa da tsaki a kan man fetur na ci gaba da yin tsokaci game da cire tallafin mai da ya janyo tankiya tsakanin gwamnati da 'yan kwadago
Sabon Gwamnan Jijar Neja a Nigeria Umar Muhammed Bago tare da Mataimakinsa Kwamred Yakubu Garba sun sha rantsuwar kama aiki a Jihar Nejan mai yawan jama’a kimanin Milyan 5.
A yanzu haka dai filin saukar jiragen sama na kasa da kasa dake birnin Minna fadar gwamnatin jihar Nejan Nigeria na cikin wani yanayi na fitar hayyaci.
Kimanin jami’an tsaron ‘yan banga biyar ne ake kyautata zaton sun mutu, ciki har da wani kwamanda guda a sakamakon wasu hare-hare da ‘yan fashin daji suka kai a jihar Neja da ke Najeriya.
Hukumar Alhazan dai ita ce ke da alhakin kai maniyyata aikin Hajji a kasa mai tsarki ta Saudiyya domin sauke farali, da kuma mabiya addinin Kirista da ke zuwa kasar Isra’ila domin yin ta su ibadar.
Kamar dai yadda bayanai suka nuna, yankin Arewacin Nigeria ya kasance koma baya a fannin ci gaban ilimin boko ko na zamani, lamarin da masana suka bayyana cewa yana daya daga cikin dalilan rashin samun bunkasar tattalin arzikin yankin kamar yadda ya kamata.
Al’ummomin dake Garin Ibbi ta karamar hukumar Mashegu a jihar Nejan Najeriya da wasu kauyukan da ke kusa dasu na cikin wani yanayi na tashin hankali tare da zaman makoki bayan da wasu ‘yan bindiga suka halaka wasu mutanen yankin, suka kuma yi garkuwa da wasu.
Gwamnatin jihar Kogi da ke arewa ta tsakiyar Najeriya, ta yi Allah wadai da mummunan harin da wasu ‘yan bindiga su ka kai da ya hallaka mutane da dama a jihar.
Al'ummar jihar Neja suna cikin tashin hankali a sakamakon harin da 'yan bindiga suke cigaba da kaiwa yankunan karkara.
Domin Kari