Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojojin Najeriya Ta Kammala Atisayen ‘Operation Mugun Bugu’ Don Yaki Da 'Yan Tada Kayar Baya


Sojojin Najeriya (Facebook/Rundunar sojin Najeriya)
Sojojin Najeriya (Facebook/Rundunar sojin Najeriya)

Rundunar sojojin Najeriya ta kammala wani atisayen makwanni biyu da ta yi wa lakabi da “Operation Mugun Bugu” wanda shine na biyu a wannan shekara ta 2023.

Dakarun rundunar sun yi gwajin makamai a babban dajin barikin Soji dake garin Kontagora na jihar Naija.

Shugaban rundunar tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, wanda Manjo Janar Jal Jimoh ya wakilta, ya ce rundunar sojin sama na taimakawa rundunar sojin kasa don tabbatar da samun nasarar da ake bukata a yaki da ta’addanci.

Ya ci gaba da yin kira ga samun hadin kan ‘ya Najeriya wajen tsegunta bayanai da za su taimaka don kawar da bata gari da ke neman kawo rashin zaman lafiya a Najeriya.

Da ya ke jawabi shugaban rundunar sojin kasa ta Najeriya, Labtanal Janar Taoreed Lagbaja, wanda Manjo Janar SG Musa ya wakilta, ya ce horon da dakarunsu suka samu, ya hada da kwarewa ta musamman da za su iya tunkarar duk wani kalubale irin na rashin tsaro.

A daya bangaren kuma, masu sharhi kan lamuran tsaro irin su Dakta Yahuza Ahmed Getso, na nuna cewa duk da haka akwai bukatar rundunar ta kara samun hadin kan al’umma, kan yadda ake samun masu tseguntawa ‘yan bindiga da ke mayar da hannun agogo baya.

Domin Karin bayani saurari rahotan Mustpha Nasiru Batsari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG