A lokacin da yake ayyana sakamakon zaben, babban jami’in tattara sakamakon zaben na jihar Kogi, Farfesa Johnson Urama daga jami’ar Nsuka, ya ce Ahmed Ododo yana gaba da kuri’u 444,237.
Bisa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya shine wanda ya lashe zaben da aka gudanar.
Dan takarar jam’iyyar SDP Alhaji Murtala Ajaka, shine yazo na biyu da kuri’u 259,052.
Dan takarar babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Sanata Dino Malaye shine wanda yazo na Uku da kuri’u 46,362.
Tuni dai jam’iyyar SDP ta yi watsi da sakamakon zaben kamar yadda wakilin jam’iyyar Mista David Ahimori ya bayyana rashin gamsuwarsa, don haka ya ce za su bi tsarin doka don bin hakkinsu.
Shi kuwa wakilin APC a dakin tattara sakaamko Abdul’aziz Idris ya nuna gamsuwa ga zaben, sai dai korafi irin na masu shan kaye.
Hukumar zabe ta ce korafi da aka samu a wasu rumfunan zabe da aka soke zabensu bai shafi sakamakon zabenba. Babban jami’in a hukumar INEC, Farfesa Sani Muhammad Adam, ya ce wanda yayi nasara ya sami tazara mai nisa, saboda haka doka ta basu damar ayyana wanda ya lashe.
Wasu da dama daga cikin masu sa ido da sashen Hausa ya zanta da su, sun nuna gamsuwa da yadda zaben ya gudana sai dai wasu ‘yan kura-kurai da ya kamata INEC ta yi gyara nan gaba.
Dandalin Mu Tattauna