Takunkumin dai tare da rufe bodar kasar ta Nijar da kungiyar Ecowas ta yi ya jefa dubban yan kasahen cikin yanayi na takura tare da kara maida hannun agogo baya ta fannin tattalin arzikin kasashen biyu.
Malam Mamman Iro shi ne sakataren mulki na kungiyar yan kasar Nijar da ke zaune a Najeriya ya ce ya zuwa dai tura ta kai bango kuma kowa yana jin jiki saboda haka lokaci yayi da ya kama ta a ce an samu maslaha.
Shi ma dai shugaban kungiyar yan kasr ta Nijar mazauna jihar Neja Alhaji Danladi Aliyu, ya bukaci shugaban mulkin soja na kasar ta Nijar, Janar Abdurrahman Chane, da ya sassauto domin samun saukin lamarin saboda dubban al’umma na cikin wani mawuyacin hali.
Lamarin takunkumin dai ta rufe bodar ya shafi kananan yan kasuwa masu kasuwancin a yankin Arewacin Nigeria. A saboda haka shugaban kungiyar yan asalin jihar Kebbi dake zaune a jihar Neja, Alh.Hassan Usman Shiroro yace ya kamata a dubu halin da talakkawa ke ciki akan wannan matsala.
Mai sharhi akan lamurran yau da kullum a Najeriya, Alhaji Muhammadu Awaisu Giwa Kuta, ya ce sai hukumomin Nijar da Kkungiyar ECOWAS sun kai zuciya nesa kafin a warware wannan matsala.
Fata dai gano bakin zaren ta yadda al’ummomin kasashen biyu za su samu sa’ida.
Saurari rahoton:
Al’ummomin Kasashen Nijar Da Najeriya Na Ci Gaba Da Yin Kiraye Kirayen Ganin An Bude Bodar Kasar Nijar
Al’ummomin kasashen Jamhoriyar Nijar da Najeriya na ci gaba da yin kiraye kirayen ganin an bude bodar kasar Nijar tare da janye takunkumin da aka kakaba wa kasar ta Nijar bayan juyin mulkin da sojoji su ka yi a ranar 26 ga watan Yuli.
Neja, najeriya —
Dandalin Mu Tattauna