Kimanin Musulmi miliyan biyu daga kasashen duniya dari da sittin ke shirin hawan Arafah a shekarar 2023. Ranar Arfa dai ita ce mafi muhimmanci a aikin Hajji.
Wannan karon shi ne aikin Hajji da ya fi samun jama’a tun bayan dawowa daga hutun dole a sakamakon barkewar annobar cutar Coronavirus da ta addabi duniya.
Jaridar Gazzete da ake bugawa a kasar Saudiyya, ta ambaci ministan kula da aikin Hajji da Umara na kasar Dr. Taufiq Al’rabiah ya na cewa a aikin Hajji na shekara ta 2023, an janye duk wasu ka’idodi da suka shafi cutar Coronavirus.
Tuni dai suma sauran Alhazan Najeriya da suka halarci aikin Hajjin suka ce sun shirya tsayuwar Arfa ta ranar Talata.
Muhammad Awwal Aliyu, sakataren hukumar Alhazan jihar Neja a Najeriya, ya fadi cewa sun shirya motoci domin daukar Alhazan Najeriya da kuma fita da wuri saboda rage cunkoso.
Batun addu’ar neman zaman lafiya da arzikin kasa na daga cikin abin da Alhazan na Najeriya ke da niyyar roka a filin Arfa, musamman manoma a wannan lokacin na damina.
Saurari cikakken rahoton daga Mustapha Nasiru Batsari: