NIGER, NIGERIA - Wannan dai wata alamace dake nuna jihar Nejan nason bin sahun jihohin dake samar da albarkatun mai a kudancin Najeriya, dake samun kulawa ta musamman daga gwamnatin kasar.
Gwamnatin jihar Neja ta ce daga filinta ne aka samar da Abuja fadar gwamnatin Najeriya, amma kuma babu wani amfani da take samu daga wannan, sannan ga tashoshin samar da wutar lantarki guda hudu da suka hada da Shiroro, Jebba, da Kainji, yanzu kuma ga na Zungeru ana dab da kammalawa.
A lokacin da ya karbi bakuncin shugaban hukumar kula da yan gudun hijira ta Najeriya Alhaji Tijjani Aliyu, Gwamnan jjhar Nejan Umar Muhammed Bago, ya ce al’ummar jihar Neja na shan bakar wahala a kusan duk shekara ba tare da samun wata kulawa ba duk da gudummuwar da kasarsu ke bayarwa.
Alhaji Ibrahim Bolagi sakataren labaran Gwamnan Neja, ya ce yanzu fa kan mage ya waye saboda zasu bi hakkin jama’arsu ne.
Masanin kundin tsarin mulkin Najeriya lauya Mainasara Kogo Umar ya ce duk Gwamnan na da damar bin hakkinsu, amma kamata ya yi Gwamnonin da abin ya shafa su hada kai.
Madatsun ruwan dai sun shafi jihohin Kebbi,da kwara,da Neja da kuma jihar Kogi.
Saurari cikakken rahoto daga Mustapha Nasiru Batsari:
Dandalin Mu Tattauna