A yanzu haka dai garuruwa da dama dake yankin tushen lantarkin suke zama cikin duhu sakamakon rashin wutar lantarki a gabar madatsar ruwan kainji da Shiroro dake samar da lantarki a Nigeria,
Bayanai sun nuna cewa, baya ga rashin samun hasken lantarki, garuruwan suna fuskantar matsalar ambaliyar ruwa wadda ke haddasa masu tabka asarar dukiya, har ma da rayukan jamma'a kusan duk shekara A hirar shi da Muryar Amurka, wani mazaunin garin Alhaji Usman Jibirin Erana yankin tashar ruwan dake samar da lantarki a shiroro ya bayyana cewa, suna fama da matsalar ambaliya a sakamakon bude madatsar ruwan na Shiroro, amma basu taba samun kulawa daga hukumomin tashar ba.
Shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi ta jihar Neja kuma Shugaban karamar Hukumar Borgu, inda tashar samar da lantarki ta Kinji take Alh.Yarima Kilishi Suleman yace suna kokarin karbowa mutanen su hakkin su daga damfanonin samar da wutar lantarki, amma har yanzu lamarin bai samu ba.
Ko da yake dai duk wani kokari da aka yi don jin ta bakin wani daga cikin jami'an kamfanonin samar da wutar lantarki dake wadannan wurare yaci tura, shugaban hukumar mai kula da garuruwan dake samar da lantarki a Nigeria HYPADEC Alh. Abubakar sadik, Katukan Yawuri, ya shaida cewa, a baya an samu matsaloli amma yanzu anyi gyara kuma nan ba da jimawa ba za a gani a kasa.
Gwamnan jihar Nejan Alh. Umar Muhammed Bago, bayan da ya karbi bakuncin tawagar hukumar ta HYPADEC, bai yi wani karin haske a game da ziyarar tasu ba sosai a lokacin da aka yi mishi tambaya akan wannan al'amarin
Sai dai kuma, Gwamna Bago ya bukaci hukumar ta HYPADEC ta kara himma wajen bunkasa rayuwar al'ummomin wadannan yankuna domin rage masu radadin wahal-halun da suke fuskanta.
Saurari cikaken rahoton Mustapha Nasiru Batsari daga Neja:
Dandalin Mu Tattauna