Kawowa lokacin hada wannan rahoto dai babu wani labari mara dadi game da yadda zaben ke tafiya daga sassan jihar Kogin, sai dai korafe-korafen yin ba dai-dai ba a wasu yankunan karkara na jihar Kogin.
A yankin Jikko kusa da Asawa ta karamar hukumar Lokoja, akwai labarin hana masu zaben kada kuri’arsu bayan an tantancesu. Malam Muhammadu Garba dake zaune a yankin ya ce suna da yawa da a ka yi ma hakanan a ciki har da ma shugabansu.
A cikin garin Lokoja, maza da mata da Muryar Amurka ta zanta da su sun nuna gamsuwa da yadda zaben ke gudana.
Shugaban Jam’iyyar APC a yankin Lokoja ya musanta labarin cewa suna sayen kuri’un jama’a da kudi.
Shima shugaban hukumar bada ilimi bai daya a jihar Kogin Alh. Suleman Abdullahi ya bukaci ‘yan siyasar da su rungumi kaddara a duk yadda sakamakon zaben ya kasance.
Zaben na jihar Kogi dai a na yin shine cikin yanayi na zaman makokin mutuwar shugaban karamar hukumar Lokoja Alh. Muhammadu Dan Asabe wanda ya yanke jiki ya fadi ya mutu kwana daya kafin gudanar da zaben.
Saurari rahoton:
Dandalin Mu Tattauna