NIGER, NIGERIA - Tun a shekarar 1990 ne alokacin mulkin soja na Janar Ibrahim Badamasi Babangida aka kaddamar da wannan filin jirgin sama a kauyen Maikunkele da ke kusa da Minna.
To sai dai a yanzu haka filin jirgin ya share shekaru hudu yana cikin wani yanayi mara kyau. Al’amarin da ya jefa matafiya ta sama musamman masu tafiya aikin Hajji da kuma Kiristoci masu zuwa ibada kasar Isra’ila cikin damuwa da tashin hankali.
Amirul Hajji na wannan shekara ta 2023 a jihar Neja kuma Sarkin Borgu Alhaji Sani Halliru Dantoro ya ce duk da yake suna fatan ganin an kwashe Alhazan jihar Nejan daga Minna amma lamarin zai yi wuya.
Hukumomin dake kula da wannan filin jirgin sama sun ce suna kokarin gyara abubuwa da dama da suka bar aiki a wuri.
Ko a baya zirga-zirgar masu Ibada a filin jirgin na Minna tamkar mataimaki ne ga babban filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja kasancewar shine filin jirgi mafi kusa da Abujan.
Saurari cikakken rahoto daga Mustapha Nasiru Batsari: