Hukumar Alhazai ta kasa ta ce za ta hada kai da hukumomin Alhazai na jihohi wajen jan hankalin maniyata kan sabbin tsare-tsare da kasar Saudi Arabiya ta bullo da su, domin gudanar da aikin hajjin shekara mai zuwa.
Kawo yanzu kotun daukaka kararrakin zabe a jihohin kasar ta kori yan Majalisar dattawa 7 da na wakilai 26, kuma har yanzu ba a gama ba tukunna.
Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Kingsley Moghalu, ya yi kiran da a rage albashi da alawus-alawus na masu rike da mukaman siyasa har da na ‘yan majalisar dokokin kasar da kashi 50 cikin 100.
Ma'aikatar Jinkai da Rage radaddin talauci ta ce ta samu wasu makudan kudade a binciken da ta ke gudanarwa, saboda haka ta shirya biyan 'YAN BATCH C' wadanda ke bin bashin alawus din su har na tsawon wattani 9.
Majalisar Dattawan Najeriya ta yi kwaskwarima ga dokar hukumar kula da Zuba Jari ta kasa wacce aka fi sani da NSIP, da nufin dauke hukumar daga ma'aikatar agaji da rage talauci zuwa fadar shugaban kasa. Amma kwararre a fannin zamantakewar bil'adama na ganin abin ba zai canja zani ba.
A safiyar ranar Litinin ne wani labari da ba a san inda ya samo asali ba ya yadu a dandalin sada zumunta cewa tsohon Shugaban Najeriya a zamanin mulkin soja, Janar Yakubu Jack Gowon mai murabus ya riga mu gidan gaskiya.
'Yan Najeriya sama da miliyan daya ne za su rasa ayyukanşu a karkashin shirin tallafin yaye talauci na N-Power na Gwamnatin tarayyya, biyo bayan dakatar da shirin da Gwamnati ta yi na tsawon lokaci.
Bankin Duniya ya wallafa wani rahoto da ke cewa tun daga tsakiyar watan Yuni na shekarar 2023 darajar Naira ta ragu da kashi 40 cikin 100. Wannan ya nuna cewa naira ta zama kudi mafi lalacewa a cikin kudaden da ake kasuwanci da su a kasashen Afirka. Masana sun tofa albarkacin bakinsu.
Cikin dalilan akwai batun ba iyalai miliyan 15 Naira dubu 25,000 daga watan nan na Oktoba zuwa watan Disamba na 2023, amma kungiyoyin kwadagon sun ce suna jira su ga an cika alkawari nan da wata daya in ba haka ba za su ci gaba da yajin aiki.
Majalisar dattawa ta yi wa dokar ta na gudanarwa gyaran fuska, inda aka hana sanatocin farko yin takarar kujeran Shugaban Majalisar dattawa da na mataimakinsa.
Gwamnatin Tarayya da Kungiyoyin Kwadago sun tashi daga taron da suka yi a ranar Lahadi inda suka cimma matsaya kan cewa dukkan ma'aikata za su ci gajiyar karin albashi na wucin gadi da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana a jawabin da ya yi wa kasa, yayin bikin tunawa da ranar samun 'yancin kai.
Shugaban Hukumar Mohammed Bello Shehu ya ce Hukumar ba ta samu wani umurni na kara wa Manyan Ma'aikatan Gwamnati albashi a yanzu ba, sai zuwa gaba kadan.
Wasu Kungiyoyin Fulani makiyaya a karkashin Dokta Mohammed Bello Khalil sun yi kira ga Gwamnati Tarayya da ta yi maza ta kafa masu ma'aikatar ta makiyaya.
Kungiyar amintattu da aka nada domin sa baki a takaddamar shugabanci na Kungiyar direbobi ta Najeriya NURTW ta ce ta shirya tsaf domin warware rikicin da ya taso har aka rasa ran mutum daya.
Ce-ce-ku-cen ya biyo bayan raba mukaman kwamitoci da Akpabio ya yi da kuma yadda ake zarginsa da yin subul-da-baka yayin gudanar da zaman Majalisar.
Domin Kari