Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawa Ta Rantsar Da Lalong a Matsayin Sanata Mai Wakiltan Filato Ta Kudu

Majalisa ta rantsar Simon Bako Lalong, a matsayin Sanata Mai wakiltan Filato ta Kudu a Majalisar Dattawa.
Majalisa ta rantsar Simon Bako Lalong, a matsayin Sanata Mai wakiltan Filato ta Kudu a Majalisar Dattawa.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya rantsar da tsohon Gwamnan Jihar Filato kuma Tsohon Ministan Kwadago da Samar da Aiyukan yi,  Barista Simon Bako Lalong, a matsayin Sanata mai wakiltan Filato ta Kudu a Majalisar Dattawa.

Lalong ya samu rakiyar Shugaban Jamiyyar APC na kasa,Abdullahi Ganduje, yayin rantsar da shi da misalin karfe 11.57 na safe agogon Najeriya.

Tafiyar Lalong zuwa Majalisar Dattawa ta biyo bayan hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke na tabbatar da shi a matsayin sanata.

Majalisa ta rantsar da Simon Bako Lalong, a matsayin Sanata Mai wakiltan Filato ta Kudu a Majalisar Dattawa.
Majalisa ta rantsar da Simon Bako Lalong, a matsayin Sanata Mai wakiltan Filato ta Kudu a Majalisar Dattawa.

Tunda farko dai Hukumar Zabe Mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana, Napoleon Bali, dan takarar jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 148,844 yayin da Lalong ya samu kuri’u 91,674 a zaben.

Da yake kalubalantar nasarar da Bali ya samu, Lalong ya garzaya Kotun Sauraran Kararrakin Zabe, yana mai cewa PDP ba ta da tsarin da ya dace wurin tsayar da dan takaranta.

Majalisa ta rantsar da Simon Bako Lalong, a matsayin Sanata mai wakiltan Filato ta Kudu a Majalisar Dattawa.
Majalisa ta rantsar da Simon Bako Lalong, a matsayin Sanata mai wakiltan Filato ta Kudu a Majalisar Dattawa.

A hukunci da Mai Shari’a Muhammad Tukur ya yanke, kotun ta soke nasarar da Bali ya samu da kuri’un da ya samu a zaben.

Bali ya daukaka kara zuwa Kotun Daukaka Kara, karkashin jagorancin Mai Shari’a Elfrieda Williams-Dawodu, amma duk da zanga-zangar da PDP ta yi, kotun daukaka kara ta sake tabbatar da Lalong a matsayin halastaccen Sanatan yankin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG