Manazarta na hasashen cewa wannan zai zama karon farko da za'a sami irin yawan yan majalisa da aka kora tun dawowar tafarkin dimokradiya a shekarar 1999.
A yayin da jamiyyar APC mai mulki ta kasance ta fi kowa cin gajiyar hukunce-hukuncen da kotuna daban-daban suka yanke na kujerun yan majalisar wakilai, jamiyyar ta yi asarar kujerun sanatoci fiye da kowacce jamiyyar kawo yanzu.
Sai dai duk wadanda suka rasa kujerunsu, sun bayyana aniyarsu ta cewa za su daukaka kara kan hukuncin.
Kotun ta soke nasarar da jamiyya mai mulki ta yi a yankuna Kogi ta gabas da kuma Kogi ta tsakiya. Haka kuma ta samu nasarar lashe zabe a yankunan Delta ta tsakiya da kuma Delta ta Kudu.
Sai Kotun daukaka kara da ta soke zaben Adamawa ta Arewa inda ta ba da umurnin sake zabe a Filato ta Arewa wanda Simon Mwadkwon na Jamiyyar PDP ya lashe a ranan 25 ga watan Febrairun wannan shekara.
Wani dan jamiyyar PDP a jihar Filato Emmanuel Macham ya ce wannan abin da ya faru a jamiyyar PDP ba su same shi da sauki ba, a yanzu suna cikin zaman makoki kan wannan abu da ya faru a kotun daukaka kara a Abuja inda aka soke zaben dan majalisar jam'iyyar, wanda shi ne Shugaban marasa rinjaye a Majalisar dattawa.
Macham ya ce wannan abin ya auku ne saboda abubuwa da dama da suka faru a jam'iyyar da ba su tafi daidai ba saboda jamiyyar ta rabu kashi-kashi. Macham ya ce dole ne jamiyyar PDP ta dawo kan tebur domin neman mafita.
Amma a bangaren APC kuma, tsohon Sakataren Jamiyyar a Pilato Bashir Musa Sati ya ce wannan hukunci ya yi masu dadi, domin ya nuna cewa jamiyyar APC za ta iya samun nasara a zaben da za a sake yi nan da kwanaki kusan 90.
Sati ya ce sun gamsu da hukuncin kuma a shirye suke su shiga zabe da karfin su.
Shugaban tsangayar kimiyar siyasa da alaka ta kasa da kasa na Jami'ar Abuja Farfesa Sherif Ghali Ibrahim, ya yi tsokaci cewa wadannan hukunce hukunce da aka yi kan 'yan majalisu ya zama kamar an shiga wata guguwa ce babba, wacce ta zama tsumagiyar kan hanya, fyade yaro-fyade babba.
Sherif ya ce "babbar matsalar mu a wannan kasa shi ne bangaren shari'a. Daga dukan alamu suna bari a yi masu katsalandan a harkokin su na shari'a musamman ma na harkokin zabe. Irin wannan hukunci da kotu ta yanke kan shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa, yana nuni da cewa wanda aka cire zai iya sake tsayawa takara a bisa doka.
Shi kuwa tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa Forfesa Attahiru Jega, ya ce idan ana so a ga tsafta a harkokin zabe, to sai an dauki mataki na gyara dokar zabe wajen amincewa da yin amfani da na'ura wajen bayyana sakamakon zabe da makamancin haka.
Jega ya ce wannan mataki zai iya kawo tsafta a harkar zabe, har ya rage yawan kace-na-ce da ke tasowa a kullum.
Ya zuwa lokacin daukan wannan rahoto, jamiyyar PDP ta rasa mambobi 12 a majalisar, sannan kuma Jamiyyar lebo ce ke bi mata da mambobi 10, yayin da Jamiyyar NNPP na da mambobi uku sai APC mai mamba daya.
Saurari rahoton:
Dandalin Mu Tattauna