Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun ECOWAS Ta Yi Watsi Da Bukatar Nijar Na Janye Ma Ta Takunkumi


ECOWAS
ECOWAS

Da ya ke yanke hukunci a ranar Alhamis, mai shari'a Dupe Atoki ya kira gwamnatin sojin Nijar da haramtacciya, wadda ta saba wa kundin tsarin mulkin Nijar, saboda haka ba'a amince da ita a matsayin mamba a kungiyar kasashen yankin ba.

Tun bayan juyin mulkin da ya hambarar da shugaban kasar Nijar Mohammed Bazoum a watan Yulin shekarar 2023, kungiyar hadin kan tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma ECOWAS, ta sanya wa Nijar din takunkumai da suka hada da rufe kan iyakokin kasar, da dakatar da hada-hadar kudi da kuma rufe kadarorin kasar da ke kasashen kungiyar.

A matsayin goyon bayan hukuncin na ECOWAS, Najeriya ta katse wutar lantarki da ke samar da kashi 70 cikin 100 na wutar lantarki a Nijar.

A karar da ta shigar, Nijar ta kalubalanci takunkuman da kungiyar Ecowas din ta kakaba ma ta, inda ta nuna cewa matakin ya janyo wa 'yan kasar shiga wani mawuyacin hali da ya hada da karancin abinci da magunguna a asibitocin kasar.

Da ya ke yanke hukunci a ranar Alhamis, mai shari'a Dupe Atoki ya kira gwamnatin sojin Nijar da haramtacciya, wadda ta saba wa kundin tsarin mulkin Nijar, saboda haka ba'a amince da ita a matsayin mamba a kungiyar kasashen yankin ba.

Barista Oumarou Kadiri shi ne lauyan gwamnatin kasar Nijar, ya ce suna jira su ga takardar da kotu za ta ba su da bayanin abin da ake nufi da yin watsi da karar. Oumaru ya ce sun shigar da kara ne a matsayin kasa da aka kakabawa takunkumin da ke wahalar da 'yan kasar ta. Oumaru ya ce in sun sami takardar za su yi nazari a kan ta.

A lokacin da yake mayar da martani kan hukuncin, shugaban yan Nijar mazauna Najeriya Abubakar Khalidu ya yi bayani cewa kotu ba ta yi wa yan Nijar adalci ba duk da cewa shari'a sabanin hankali ce.

Khalidu ya ce irin takunkumin da aka sa wa Nijar ya yi tsauri sosai, yana mai bayyana ra'ayin cewa takunkumin da ya kamata a sa shi ne na hana masu laifi tafiye-tafiye, maimakon takura wa kasa baki daya.

Ya ce takunkumin ya shafi bangaren kasuwanci, da shige-da-fice wanda a yanzu sai ta barauniyar hanya ake bi zuwa Nijar daga Najeriya. Ya kara da cewa kamata ya yi kotu ta duba 'yan kasa da abubuwan da suke bukata.

Saurari cikakken rahoton Medina Dauda:

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG