Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Yi Kira Ga MDD Ta Shiga Tsakanin Rikicin Isra’ila Da Falasdinu


ISRAEL-HAMAS
ISRAEL-HAMAS

Majalisar Dattawan Najeriya ta yi wani zama na musamman kan rikicin Isra'ila da Falesdinu, inda ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta dauki matakin gaggawa wajen kawo karshen rikicin.

ABUJA, NIGERIA - Haka kuma wasu shugabanin manyan addinai guda biyu na kasar, sun goyi bayan wannan kira.

Wannan shine karon farko da Majalisar Dattawan Najeriya ta yi kira da a kawo karshen yakin Isra'ila da Hamas da ya yi sanadiyar mutiwar dubban mutane.

Majalisar dattawan ta kuma bukaci bangaren zartaswa na gwamnati da su shiga cikin rikicin ta hanyar kiran kasashen biyu daban daban na Isra'ila da Falasdinu da su tsagaita wuta. Hakan ya biyo bayan amincewa da kudurin da Sanata Suleiman Kawu Sumaila ya dauki nauyi da shi da wasu Sanatoci 28 da suka mara masa baya.

Kawu ya ce tun da wanan yaki ya barke, alkaluman mutane da aka kashe abu ne mai ban tsoro, kuma idan ba a kawo karshen yakin ba zai iya komawa ya zama yakin duniya na uku. Kawu ya ce idan haka ya faru, to zai shafi duniya baki daya, shi yasa Majalisa ta amince da kudurin da ya kawo aka yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta hanzarta kawo karshen yakin tun da wuri. Kawu ya ce a raba kasashen a ba kowa kasar sa, kuma kar a bari wani ya rika shiga kasar wani.

Shi ma daya cikin sanatocin da suka goyi bayan kudurin, Sanata Iqra Aliyu Bilbis ya ce ganin yadda yakin ya rika kashe yara kanan da mata da tsofafi ya sa dole ne wani mai tausayi yayi kira da a hanzarta kai kayan agaji ga mabukata. Bilbis ya ce Allah ne ya halice mu baki daya kuma ya ba kowa 'yanci. Bilbis yayi kira ga Najeriya da ta hada hannu da sauran kasashe wajen kawo karshen rikicin tare da neman a kai kayan agajin cikin gaggawa domin a kawo wa mabukata sauki.

A bangaren manyan addinan biyu da ake da su a Najeriya, Musulunci da Kiristanci, Jami'i a Majalisar Koli ta Shari'a Aminu Inuwa Mohammed ya yi tsokaci cewa wannan abu da ke faruwa a zirin Gaza abu ne da ake yi tun shekaru sama da arba'in amma wanda ake yi a kwanannan shi ne ya fi zafi, domin ana ta kashe mutane da basu san hawa ba ba su san sauka ba musamman ma yara kanan da mata.

Saboda haka su na fata cewa Najeriya za ta dauki kwakwarar mataki wajen bada gudunmawa mai tsoka domin a ba mabukata agaji musamman ma a zirin Gaza inda kashe kashen ya fi yawa. Aminu ya ce akwai tsari na Majalisar Dinkin Duniya da ya ba kowa dama na zama inda yake so, Majalisar Shari'a tana so a koma wannan tsarin domin kuwa ya tsuguna inda Allah ya ajiye shi.

Shi ma sakataren kungiyar CAN ta Arewa ta tsakiya Pastor Simon A. S. Dolly ya ce yana goyon bayan matakin da Majalisar Dattawa ta dauka dari bisa dari kan abinda Majalisar Dattawa suka yi. Dolly ya ce kashe kashe da ake yi a Gaza bai dace ba domin yara da mata ne ake ta kashewa wadanda ba su ji ba basu gani ba.

Dolly ya ce ba suna goyon bayan matakin harin da Hamas suka kai wa Israila ba ne, amma wannan kashe kashe ya yi yawa sosai. Saboda haka yana kira ga manyan addinan kasar da su ci gaba da yin addu'a na kawo karshen wanan yaki. Dolly ya ce Majalisar Dinkin Duniya ta yi dukanin mai yiwuwa wajen kawo karshen wannan yaki.

Alkaluman Majalisar Dinkin Duniya kan yakin da ya barke a watan Oktoba inda kungiyar Hamas ta kai hari kan Isra'ila na nuni da cewa an lalata wuraren ibada 18, da wuraren zama 22,600 da cibiyoyin kiwon lafiya 19, da cibiyoyin ilimi 90, masana'antu 70 da ofisoshin watsa labarai 49.

Saurari cikakken rahoto daga Medina Dauda:

Majalisar Dattawa Najeriya Ta Yi Kira Ga MDD Ta Shiga Tsakanin Rikicin Isra’ila Da Faladinu.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:31 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG