Majalisar Dokokin Najeriya ta ba da hujjar da ya sa ta daga kasafin kudin da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya mika mata daga Naira Tiriliyan 27.5 zuwa Naira Tiriliyan 28.7 inda Majalisar ta ce lallai za ta sa ido ta tabbatar an yi wa yan kasa aiki da kasafin kudin.
Kasafin kudin wanda majalisar dattawa da ta wakilai suka amince da shi, ya zo ne bayan kwamitocin kula da kasafin kudin suka gabatar da rahoto cewa, sun bi kasafin daki-daki domin gudun kuskure.
Mataimakin shugaban Kwamitin Kasafi na Majalisar Dattawa, Sanata Mohammed Ali Ndume, ya yi nazari cewa, sun yi aiki tukuru, babu dare babu rana domin sun gano wurin da aka yi ta jita-jita cewa, an fifita yankin kudu kan yankin arewa a kasafin kudin.
Ndume ya yi bayani cewa wannan ce-ce-kuce da ya taso kan kasafin cewa an fifita yankin kudu kan yankin arewa karya ce kawai, domin yawancin wadanda ke bita kan kasafin kudin kasa a majalisar dokoki dukan su ‘yan Arewa ne, saboda haka zai yi wuya su bari a yi wa Arewa kafar ANgulu.
Ndume ya kara da cewa duniya ta ci gaba, saboda akwai hanyoyi da yawa na yin bincike ta na'ura mai aiki da kwakwalwa, ga kuma sabuwa wace ake cema AI, yanzu yanzu za ta budo maka duk abin da ke boye.
“Za mu sa ido mu ga yadda za’a aiwatar da kasafin daki-daki,” in ji Ndume.
A lokacin da yake wa manema labarai Karin bayani, shugaban kwamitin kula da kasafin kudi a majalisar wakilai, Abubakar Kabir Bichi, ya ba da hujjar karin kudin, sannan ya ce an toshe gibin korafe-korafen da Jihohi suka yi kan Kasafin Kudin
Bichi ya ce an kara kudin ne domin an samu karuwar hauhawar farashin kayayyaki, da kuma alkawarin da kamfanonin gwamnati suka yi na kara Kudaden shiga zuwa Naira biliyan 700.
Akwai hauhawar farashin dala da kuma chanjin dala, saboda haka suka kara farsahin dala daga 759 da Shugaban kasa ya kawo zuwa Naira 800 kan dala daya, a cewar Bichi.
Amma masanin tattalin arziki, Shuaibu Idris Mikati, ya ce akwai abin dubawa kan yadda kasafin kudin ya zo inda ya ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta so kanta da yawa, domin kasuwar mai babu wanda zai iya sanin gobe sai Allah.
Mikati ya ce kudin gangar danyen man fetur yana iya tashi ko ya sauka, idan an bar shi a yadda shugaban kasa ya kawo a kasafin kudin, zai iya kawo cikas a bangaren samun kudaden shiga. Saboda haka Majalisa sun yi daidai da suka yi karin kudin.
Majalisa za ta mika wa Shugaban kasa Kasafin kudin domin ya sa hannu saboda a fara aiwatarwa a watan Janairun nan mai kamawa.
Saurari cikakken rahoton Medina Dauda:
Dandalin Mu Tattauna