Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Najeriya Ta Yi Kira Ga Ma’aikatun Gwamnati Su Zarta Kasafin Kudin Badi


Taron yan majalisa da sanatoci da aka yi a hade
Taron yan majalisa da sanatoci da aka yi a hade

Kwamitin Kudi a Majalisar Dokokin Kasa ya yi kira ga hukumomi da ma'aikatun gwamnati masu samar da kudaden shiga su yi kokarin wuce abinda aka kawo a kundin kasafin kudin badi.

Wanan na zuwa ne bayan da Majalisar ta tabbatar da an ware Naira triliyan 18.324 a matsayin kudin shiga daga jimlar kudin da za a kashe na Naira triliyan 27.503. Amma kuma akwai gibin Naira triliyan 9.18 da dole a cike shi.

A zaman da aka gudanar kan kasafin kudin, a karkashin shugaban kwamitin kudi na Majalisar dattawa, Sanata Mohammed Sani Musa, an tantance shirye - shirye da manufofin wadannan hukumomi da tunanin mai yiwuwa su fuskanci kalubalen kudi a badi, inda aka ba su shawarar su yi kokarin wuce wadannan manufofin domin kasafin kudin na shekara mai zuwa ya ta'allaka ne kan hada rancen kudi daga cikin gida da waje, da kuma kudaden da ake samu daga mayar da hannun jari don cike gibin da ake hasashe.

Da ya ke tsokaci kan batun, Ministan Kula da Kasafin Kudi Wale Edun ya yi amanna da shawarwarin 'yan majalisar, inda ya ce mai yiwu ne, gwamnatin tarayya za ta kawo bukata kara yawan kasafin kudin shekara 2024, amma idan ta samu karin kudaden shiga da ta aiyyana za ta samu.

Saurari cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:02 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG