Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokoki Sun Amince Shugaba Tinubu Ya Ciwo Bashin Naira Tiriliyan 7.5


Majalisar Dokokin Najeriya (Twitter/National Assembly)
Majalisar Dokokin Najeriya (Twitter/National Assembly)

Majalisar Dokokin Najeriya ta sake amincewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ciwo wasu bashi da ya kai Dalar Amurka Biliyan 8.2, kwatankwacin Naira triliyan 7.5 domin lamuni na dogon zango.

Shugaban Kwamitin Kula da Kasafin Kudi a Majalisar Dattawa, Mohammed Sani Musa, ya ce sun amince da wadannan bukatu na Shugaban kasa ne bayan sun saurari ba'asi daga wurin jama'a, kuma amincewa da tsarin zai zama wata hanya ce da za ta bada dama na amfani da na'urar zamani wajen gane abubuwa da yadda za a aiwatar da kudaden.

Hakazalika, mataimakinsa, Mohammed Ali Ndume, ya yi karin haske cewa a cikin kasafin kudin badi aka kawo wannan bukata kuma sun amince masa da wannan sauyi na mayar da kudaden asusun lamuni domin wannan shi ne kasafin kudin Shugaba Tinubu na farko, kuma ba sa so a ga kaman sun hana ruwa gudu, saboda haka za su tabbatar da sa ido a yadda wannan tsari zai tabbata, tare da fatan zai zame wa kasa alheri.

Mataimakin Shugaban Kwamitin Kula da Kasafin Kudi a Majalisar Dattawa, Mohammed Ali Ndume
Mataimakin Shugaban Kwamitin Kula da Kasafin Kudi a Majalisar Dattawa, Mohammed Ali Ndume

Shi kuwa Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi a Majalisar Wakilai, Abubakar Bichi, ya yaba da tsarin inda ya ce wannan sauyi da aka yi wajen tantance Kasafin kudin da bin matakai daki daki zai kawo wa kasa cigaba wajen samu aikace aikace irin su titunan sufuri, da harkar noma, da ciyar da yara a makarantu da sauran abubuwa da talaka zai amfana. Bichi ya ce akwai kyakyawar fata na cewa za a ga sauyi sosai a rayuwar alu'mma tunda shugaban kasa ya riga ya sa wa kasafin kudin hannu.

Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi a Majalisar Wakilai, Abubakar Bichi
Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi a Majalisar Wakilai, Abubakar Bichi

Kafin wannan karin, kasa tana da bashi har na Naira Triliyan 87.38, wanda idan an hada da wannan, basussukan za su iya kaiwa tirilyan 100 ko fiye a cikin dan gajeren lokaci, duk da cewa Shugaba Tinubu ya yi wa majalisar bayanin cewa sauya shekar zuwa lamuni zai rage kudin biyan basussukan zuwa kashi 9 cikin 100 idan an kwatanta da tsarin hada hadar kudi wanda ake karba a yanzu wanda ya kama kashi 3 cikin 100.

Hakan dai wani abu ne da masanan tattalin arziki ke cewa yawan bashi zai hana kasar samun kudaden shiga da za su kawo wa talaka wata cigaba mai ma'ana.

Yusha'u Aliyu, yana kira ne da a yi taka tsantsan kan basussukan wannan ya nuna cewa kasafin kudin da Gwamnatin taraiyya ta gabatar, kasafi ne mai gibi, saboda haka duk abubuwan da aka tanadar domin gina kasa zai zama yana da wahala, kuma zai iya kawo tarnaki wajen kudaden da za a tara domin cigaban kasa.

Wani rahoto da ya fito daga shafin Darakta Janar na Ofishin Kasafin Kudi, Ben Akabueze, ya ce Gwamnatin Taraiyya ta cire hukumomi 26 daga cikin kasafin kudinta na wannan shekara a matsayin wata manufa na cimma tsarin ceton kudi.

Ga nan cikakken rahoton Medina Dauda da ga Abuja, Najeriya

Majalisar Dokoki Sun Amince Shugaba Tinubu Ya Ciwo Bashin Naira Tiriliyan 7.5
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:49 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG