Majalisar Wakilai na neman a amince da kudin kasar Sin--Yuan--ya zama daya dag cikin kudaden kasar waje da ake ajiyar su a hukumance.
Amma masanan tattalin arziki na bayyana ra'ayoyi mabanbanta kan alfanun hakan ga kasar.
Dan Majalisa mai wakiltan Bogoro/Dass/Tafawa Balewa ta Jihar Bauchi, Jafaru Gambo Leko ne ya kawo wannan kudiri a zauren Majalisar ta Wakilai kuma aka amince da Kudurin.
Jafaru ya ja hankalin majalisar kan yadda tattalin arzikin Najeriya ya fuskanci sauye-sauye masu yawa a game da darajar Naira, wanda hakan ya haifar da tabarbarewar tattalin arziki da rashin tabbas.
Hakan ya sa majalisar ta umarci kwamitocinta masu kula da Bankuna da harkokin Kudade, da su tattauna da babban bankin Najeriya-CBN don su lalubo hanyoyin da suka dace da manufofi da za su taimaka wajen ganin Najeriy ta fara amfani da kudin China na Yuan don gudanar da kasuwanci.
Jafaru ya yi karin bayani cewa ya lura da yadda Dalar Amurka ta zame wa ‘yan Najeriya barazana ga kasuwancinsu, har ma da rayuwarsu baki daya, shi ya sa ya gabatar da wannan kudurin.
Dan majalisar ya kara da cewa Dalar Amurka ta shafi komai na rayuwar ‘yan Najeriya inda duk abin da ake sayarwa sai a ce farashinsa ya tashi saboda tashin farashin Dala.
Jafaru ya ce hatta kayyayaki da ake nomawa a Najeriya sai a ce farashinsu ya tashi saboda tashin farashin Dalar Amurka.
Sai dai masanin tattalin arziki irinsu Yusha'u Aliyu na ganin wannan tsari, tsari ne da ya dade a cikin tattalin arzikin duniya saboda bunkasar tattalin arzikin China na kokarin ta mayar da kudin ta ya zama abin da ake cewa a turanci “International Reserve Currency,” wato kudin da kasashe za su rika ajiye wa don yin harkokin kasuwanci.
Yanzu dai Dala ce ke kan gaba kuma tana tafiyar da kusan kashi 58.47 na kudaden da ake ajiyewa domin harkar kasuwanci ko na ajiye kudi na duniya.
Yusha'u ya ce wani tsohon Gwamnan babban Banki na Najeriya ya taba yin kira da cewa dole ne Najeriya ta fara ajiye kudaden harkokin kudaden wajenta cikin kudin Yuan, kuma wannan tsari da ake ta kokari a yi bai wuce tasirin kasar China ba saboda wasu abubuwa da suka taso sababbi musamman ita Najeriya da take kokarin ta hade da wannan Kungiya wanda ake kira ‘BRICKS.
Kasashen BRICS sun hada da Brazil, Rasha, Indiya, China da Afirka ta Kudu.
Yusha'u ya ce Najeriya ta nuna lallai tana so ta shiga wannan yarjejeniya, kuma wannan yarjejeniya za ta ba Najeriya damar ta ci gaba da kasuwanci da kasar China ne saboda dama da yawa daga cikin kasuwancinta da ya hada da matatun mai da kananan masana'antu da abubuwa da suka shafi samar da ruwa da harkokin ilimi ana yin su ne da kasar China.
Shi ma dan Majalisar wakilai daga jihar Jigawa Sa'ad Wada Taura ya yi nazari kan kudurin inda ya ce duk lokacin da aka samu masana ko masu ruwa da tsaki sun kawo hasashe ko hange, ba a rasa nasaba da dalili da ya ke kawo irin wannan lamarin.
Saurari cikakken rahoton Medina Dauda:
Dandalin Mu Tattauna