Kungiyar Kwadagon ta yi barazanar sake tsunduma yajin aiki bayan gwamnatin tarayya ta dakatar da biyan ma'aikatan ta kudaden rage radadin cire tallafin mai bayan ma'aikatan sun karbi na wata daya kacal.
Shugaban sashen tsare-tsare na kungiyar kwadago ta kasa Kwamred Nasiru Kabir, ya bayyana cewa sun samu takardar dakatar da biyan 35,000, kuma dama su sun fada cewa ba su amince da biyan wadannan kudade ba tun farko.
Nasir ya ce wannan abin kunya ne gwamnati ta yi, saboda haka kungiyar kwadago ba za ta zuba ido ta ga ana zaluntar ma'aikata ba. Ya ci gaba da cewa dama kungiyar ta dan jingine yajin aikin ne ba wai ta dage ba ne, saboda haka kungiyar ta na nan daram akan bakan su babu gudu babu ja da biya.
Shugaban Muryar Talaka a Damaturu Jihar Yobe, Saleh Bakoro Sabon Feggi, ya mayar wa kungiyar Kwadago da martanin cewa karin albashi ba laifi ba ne, amma ya kamata kungiyar ta dinga yin sara tana duban bakin gatari.
Ita kuwa Lauya mai zaman kan ta Fatima Abubakar, ta yi kuka ne kan matakin da kungiyar ta ce za ta dauka, inda ta ce mutane sun gaji da batun yajin aiki da kungiyar ke barazana a ko da yaushe.
Ta kuma shawarci kungiyar kwadagon da ta nemi wata hanya ta neman hakokin jama'a ba wai ta hanyar yajin aiki kullum ba.
Wata sanarwa da kakakin Akanta Janar na Tarayya Bawa Mokwa ya fitar, na cewa gwamnati ta na kokarin biyan ma'aikatan, nan ba da jimawa ba.
Domin Karin bayani saurari rahotan Medina Dauda.
Dandalin Mu Tattauna