Yakin neman zabe na kara zafafa, a daidai lokacin da ake makon karshe kamun babban zaben.
‘Yan hamayyar a majalisar dokokin kasar sun yi wannan kiran ne saboda zargin MInistan cikin gidan da sakatarensa da nuna bangaranci a rikicin shugabancin da ake fama da shi a jam’iyar Moden Lumana ta tsohon Firai Minista Hama Amadou, zargin da suka ce ba shi da tushe.
Kasashe makwabtan Najeriya sun fara gane tasirin rawar da matasan sa-kai da ake kira Civilian JTF ke takawa wajen karya lagon ‘yan Boko Haram al'amarin da ya sa tuni wasunsu suka fara fito da nasu tsarin, wanda hakan kuma ke matukar taimakawa
'Yancin gudanar da taro cikin lumana da fadin albarkacin baki muhimman hakkokin bil'adama ne a cewar wata snaarwa daga maia'aikatar harkokin wajen Amurka.
Shugaban Amurka Donald Trump na jam’iyyar Republican da abokin adawarsa na jam’iyyar Democrat Joe Bidden sun koma yakin neman zabe ranar Juma’a 16 ga watan Oktoba bayan da kowannensu ya yi taron amsa tambayoyin masu kada kuri’a a wurare daban-daban wanda aka nuna ta talabijin.
Matar nan da Shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar don zama alkali a Kotun Kolin Amurka, Amy Coney Barret ta fuskanci jerin tambayoyi daga Sanatoci mambobin Kwamitin Majalisar Dattawan Amurka kan Harkokin Shari'a a rana ta biyu.
Kokarin kasar Saudiyya na samun kujera a Kwamitin Kare Hakkin Dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya ya ci tura duk kuwa da nasarar samun kujera da kasashe irin su China da Rasha, wadanda su ka yi kaurin suna wajen keta hakkin bil'adama.
A cigaba da shirye shiryen zaben Shugaban Kasar Amurka da ke gabatowa, da daren yau Kamala Harris Mataimakiyar dan takarar Shugaban Kasa karkashin jam'iyyar Demokarat, da Mataimakin Shugaban kasa, Mike Pence na jam'iyyar Republican, za su buga muhawara.
Burin kasar Turkiyya na zama mambar kungiyar kasashen Turai ya sake samun koma baya, bayan da kungiyar ta jefa ayar tambaya kan sahihancin tsarin demokaradiyyar da ya ke yadawa.
A cigaba da gano wasu abubuwan tayar da hankali da kungiyar IS ta gudu ta bari, a baya bayan nan an gano wasu manyan kaburbura.
A cigaba da shirye shiryen bankwana da ake ma marigayiya Ruth Bader Ginsburg ta Kotun Kolin Amurka, an fara ma ta gaisuwar girmamawa ta karshe.
A cigaba da sa ido da ake yi kan harkokin da ke gudana a Koriya Ta Arewa dangane da yawan gwaje gwajen makamai masu linzami da baje kolinsu, ana lura da yiwuwar ta kai makami mai linzami fagen fareti.
A yau Laraba aka zabi Yoshihide Suga a matsayin Firai Ministan kasar Japan. Zabansa da Majalisar Dokokin kasar su ka yi, ya biyo bayan zabensa a matsayin shugaban jam'iyyar LDP jiya Talata.
A Sudan Ta Kudu, wata gallabi tsakanin rawwuna a fagen kawo zaman lafiya, ta samu lambar yabo ta rukunin mata. Wannan ya biyo dagewar da ta yi wajen wanzar da zaman lafiya
Akwai alamar mahaukaciyar guguwar nan ta Sally za ta janyo ambaliyar ruwa idan ta karasa dannowa zuwa gabar teku a yau Laraba a Amurka.
A jamhuriyar Nijer shugabannin hukumar zaben kasar sun yi wata ganawa da wakilan jam”iyyun siyasa a karkashin inuwar majalisar warware rigingimun siyasa wato CNDP inda suka tattauna a game da inda aka kwana dangane da tsare tsaren zabukan da ke tafe.
Bayan shafe shekaru masu yawa a yaki da cutar shan inna, hukumar lafiya ta duniya ta ayyana Afrika a matsayin nahiyar da ta barranta daga cutar shan inna bayan Najeriya ta samu shekaru 4 ba tare da bullar cutar ba.
Domin Kari