Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Najeriya Sun Yi Murnar Ayyana Afrika a Matsayin Wadda Ta Rabu Da Polio


Bayan shafe shekaru masu yawa a yaki da cutar shan inna, hukumar lafiya ta duniya ta ayyana Afrika a matsayin nahiyar da ta barranta daga cutar shan inna bayan Najeriya ta samu shekaru 4 ba tare da bullar cutar ba.

Tun ziyarar tsohon sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon Najeriya a Agustan 2015, ya nuna kwarin gwiwa Najeriya mai mafi yawan jama’a a Afrika da zama mafi yawan bakar fata a duniya za ta shawo kan cutar shan inna.

Daidai watan Agustan nan an samu shekaru 4 cif da zuba ido ba tare da samun cutar ba, duk da yadda kalubalen tsaro ya kawo cikas wajen rigakafi a yankunan da Boko Haram su ka fi addaba.

Jami’in yaki da shan inna na hukuamr lafiya matakin farko a Najeriya Dr. Usman Sa'idu Adamu, ya zayyana hanyoyin da jami’an lafiya ke bi har a ka samu cimma nasarar hakan, abinda ya ce sun hada da rigakafi da zuba ido.

Rashin maida hankali tun farko kan cututtukan da a ka sani irin zazzabin cizon sauro daga masu ba da tallafi na duniya ya kawo kyamar rigakafin shan inna da wasu suka fassara da makircin Yahudawa na rage yawan jama’a.

Manyan malaman Islama irin su Sheikh Abdullahi Bala Lau na JIBWIS sun dage wajen wayar da kan jama’a, musamman bayan wani taro kan shan inna da suka halarta a Daular Larabawa.

Daraktan hukumar lafiya ta duniya a Afrika Matshidiso Moeti ta bukaci a yi takatsantsan don har yanzu Afghanistan da Pakistan na da cutar shan inna.

Tun shekaru 40 da su ka wuce da a ka samu nasarar kawar da cutar agana, sai bana a ka sake samun nasarar kawar da kwayar wata cuta.

Saurari cikakken rahoton.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00


Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG