Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamala Harris Da Mike Pence Za Su Yi Muhawara Da Daren Yau


Harris da Pence
Harris da Pence

A cigaba da shirye shiryen zaben Shugaban Kasar Amurka da ke gabatowa, da daren yau Kamala Harris Mataimakiyar dan takarar Shugaban Kasa karkashin jam'iyyar Demokarat, da Mataimakin Shugaban kasa, Mike Pence na jam'iyyar Republican, za su buga muhawara.

Muhawarar da za a yi a daren yau Laraba tsakanin Mataimakin Shugaban kasa Mike Pence da Mataimakiyar dan takarar Shugaban Kasa karkashin jam’iyyar Democrat, Kamala Harris na daga cikin jerin harkokin siyasa da annobar coronavirus ta shafa.

Kamar yadda aka saba, duk wata muhawar zaben shugaban kasa ba a cika maida hankali sosai ba kan muhawarar mataimakan akan jerin muhawarorin da ‘yan takarar shugaban kasa ke yi da yawancin lokuta ke jan hankalin masu kada kuri’a.

Amma a daidai lokacin da shugaban Amurka Donald Trump dan shekaru 74 ya kamu da corornavirus a makon da ya gabata, da kuma tsarin yakin neman zabe na taka-tsantsan da abokin adawarsa tsohon Mataimakin Shugaban kasa Joe Biden dan shekaru 77 ke yi, ta yiwu masu kada kuri’a su maida hankali akan Mataimakan ‘yan takarar da shekarunsu ke kasa da na yan takarar, wadanda zasu maye gurbinsu idan bukatar hakan ta taso.

A halin da ake ciki kuma, Shugaban Amurka Donald Trump da dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar Democrat, Joe Biden dukkansu sun fada a jiya Talata cewa sun shirya wa muhawara karo na biyu da ake shirin yi mako mai zuwa, amma batun kamuwa da coronavirus da Trump ya yi ya sa ana jefa ayar tambaya kan matakan kariyar lafiya a wurin muhawarar.

Da aka tambaye shi kan matakan kiyaye lafiya don zuwa wurin yin muhawarar, Biden ya fada wa manema labarai cewa yana fata za a bi duk matakan da ya kamata, kuma idan har Trump na da COVID a lokacin, bai kamata a yi muhawarar ba.

A na shi bangaren Trump ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, ya shirya tsaf domin karawa a muhawarar ta ranar 15 ga watan Oktoba a birnin Miami, yana mai cewa, muhawarar “za ta yi kyau.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG