Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Yi Allah Wadai Da Harbin Masu Zanga-zanga a Lagos


Mike Pompeo
Mike Pompeo

'Yancin gudanar da taro cikin lumana da fadin albarkacin baki muhimman hakkokin bil'adama ne a cewar wata snaarwa daga maia'aikatar harkokin wajen Amurka.

Da kakkausan lafazi Amurka ta yi Allah wadai da yin amfani da karfi fiye da kima da jami’an tsaron Najeriya suka yi a lokacin da suka harbi masu zanga-zanga da basa dauke da wani makami a Lagos, lamarin da ya haddasa hasarar rayuka, wasu kuma suka jikkata.

A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fidda Yau Alhamis, 22 ga watan Oktoba, Sakatare Mike Pompeo ya ce Amurka na marhabun da gudanar da bincike ba tare da bata lokaci ba akan duk wani lamari inda jami’an tsaro suka yi amfani da karfi fiye da kima. Wadanda ke da hannu a lamarin ya kamata a hukuntasu a karkashin dokokin Najeriya.

‘Yancin gudanar da taro cikin lumana da fadin albarkacin baki muhimman hakkokin bil’adama ne haka kuma muhimman abubuwa ne a tsarin dimokradiyya," a cewar sanarwar.

Amurka na yin kira ga jami’an tsaron da su mutunta hakkokin jama’a, kuma masu zanga-zanga su yi ta cikin lumana. Amurka na mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda aka kashe da wadanda lamarin ya shafa.

Facebook Forum

Labarai masu alaka

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG