Suga dan shekara 71 da haihuwa ya nuna ban girma a lokacin da 'Yan Majalisar Dokokin Japan suka zabe shi. Sakamakon kada kuri’a da aka yi yau Laraba, abu ne kusan da aka sani zai faru bayan da jam’iyyar LDP ta zabi Suga ya zama shugabanta jiya Talata.
Bisa tsarin Majalisar Dokokin Japan, jam’iyya mai mulki ce ke zaben wanda zai zama Firai Minista, yawancin lokuta Shugaban jam’iyyar ne ke zama.
Jim kadan bayan zaben sa, Suga ya gabatar da Majalisar Ministocinsa, da galibinta masu rike da mukamai ne a gwamnatin da ta shude ta Shinzo Abe, ciki harda Ministan Harkokin Wajen kasar Toshimtsu Motegi da Ministan kudin Taro Aso.
Mata biyu ne kawai a Majalisar Ministocin sabon Firai ministan.
Suga dai ya gaji mulkin kasar da tattalin arzikinta ya ji jiki sakamakon annobar coronavirus, da ta sa kan dole aka dage gasar wasannin Olympics ta Tokyo da aka dade ana jira zuwa shekarar 2021.
Facebook Forum