Kasar Saudiyya bata yi nasarar samun kujera ba a kwamitin kare hakkokin bil’adama na MDD da ake kira UNHRC a takaice a jiya Talata, amma kasashen da ake zargi da saba hakkokin bil’adama sosai ciki har da China da Rasha, sun samu nasara a kwamitin mai kasashe mambobi 47.
Zauren kwamitin, a wata kuri’ar sirri da aka akada ya zabi Bolivia, Burtaniya, China, Cuba, Faransa, Gabon, Ivory Coast, Malawi, Mexico, Nepal, Pakistan, Rasha, Senegal, Ukraine da Uzbekistan. Kasashen zasu fara wa’adin shekaru 3 daga ranar 1 ga watan Janairun shekara mai zuwa ta 2021.
Zaben da kusan aka san abinda zai faru, wanda yan takara da kungiyoyin yankuna suke gabatarwa shi ke nuna yawan yan takarar daidai da yawan kujerun. Rukuni daya kacal da aka fafata akansa sosai shine na yankin Asiya- da Pacific, inda China, Pakistan, Nepal, Uzbekistan suka kayar da Saudiyya wajen takarar kujeru hudu da suka rage.
Ana sa ran kasashen da aka zaba a kwamitin na UNHRC zasu kiyaye sharudda don karfafa tare da kare hakkokin bil’adama” a gida da waje. Kungiyoyin kare hakkokin bil’adama sun sha caccakar sabbin mambobin kwamitin sosai saboda bayanan gaza kare hakkokin bil’adama ko kuma buzantasu a kasashen.
Facebook Forum